Akwai Kura: Shugaban APC Ya Hango Matsalar da Arewa Za Ta Shiga idan Tinubu Bai Zarce ba
- Shugaban APC Nentawe Yilwatda ya ce Arewa na iya fuskantar ƙarin talauci da tsaiko ga wasu ayyukan ci gaba idan Tinubu bai sake zama shugaban ƙasa ba
- Yilwatda ya ce shirye-shiryen gwamnatin tarayya da suka shafi tituna, rance ga ɗalibai, CNG da takin zamani sun taimaka wa jihohin Arewa
- Ya kuma soki shawarar Atiku Abubakar ta dawo da tallafin man fetur, yana tambayar yadda za a samar da kuɗin ba tare da shafar sauran shirye-shirye ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi gargadin cewa yankin Arewa na iya fuskantar ƙarin talauci da koma baya idan mai girma Bola Tinubu bai samu tazarce ba.
Yilwatda ya ce wasu daga cikin shirye-shiryen gwamnatin Tinubu, ciki har da gina tituna, ba da rancen kudin karatu ga ɗalibai, shirin amfani da iskar gas wajen rage farashin sufuri (CNG) da matakan tallafa wa manoma da takin zamani, sun fi amfani ga jihohin Arewa.

Kara karanta wannan
Hutu ya kare: Shugaba Tinubu ya bar Faransa, ba zai sauka a Abuja ba idan ya dawo Najeriya

Source: Facebook
Shugaban APC ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake karɓar wasu tsofaffin ’yan ADC da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC ƙarƙashin jagorancin Princess Aslam Aliyu, cewar rahoton jaridar Daily Triust.
Yilwatda ya ce Arewa ba za ta iya komawa baya ba
Yilwatda ya ce yankin Arewa ba zai iya fuskantar komawa ga yanayin tattalin arzikin da ya ce ake ciki kafin Tinubu ya hau mulki ba.
Ya yi nuni musamman da matsalar da gwamnatocin jihohi ke fuskanta wajen biyan albashi da hakkokin fansho.
A cewarsa, wasu daga cikin manufofin gwamnatin tarayya sun samar da damar ci gaba da ayyukan more rayuwa da sauran shirye-shirye a faɗin ƙasar.
Ya tambayi yadda za a dawo da tallafin fetur
Shugaban APC ya kuma soki shawarar ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur.
Yilwatda ya tambayi yadda za a samar da kuɗin biyan tallafin ba tare da hakan ya shafi sauran shirye-shiryen gwamnati ba.
“Abin da suke ci gaba da cewa, ka sani, gidajen rediyon waje suna gaya mana cewa za su dawo da tallafin. Ni dai ina ta tambaya, ta yaya za su dawo da tallafin?” in ji shi.
Ya ce dawo da tallafin man fetur na iya yin tasiri ga kuɗaɗen da ake warewa ayyukan more rayuwa, musamman gina tituna.
Ya ce gina tituna na iya fuskantar tsaiko
Yilwatda ya tambayi ko za a dakatar da wasu ayyukan gina tituna idan gwamnati ta koma tsarin tallafin man fetur, jaridar Vanguard ta kawo labarin.
“Shin za su dakatar da duk waɗannan ayyukan gina tituna ne saboda suna son dawo da tallafin? Domin ba za a samu kuɗin ci gaba da waɗannan ayyukan ba?” in ji shi.
Ya kuma tambayi ko shirye-shiryen da aka ƙaddamar domin rage kuɗin sufuri da inganta samar da makamashi za su ci gaba idan aka dawo da tsarin tallafin.
Ya ce Arewa na buƙatar gas da takin zamani Yilwatda ya danganta manufofin gwamnatin tarayya na makamashi da bunƙasar noma a Arewa.
Ya ce yankin na buƙatar shirye-shiryen gwamnati da suka shafi samar da iskar gas da takin zamani domin tallafa wa noma.
“Wannan gas ɗin zai tafi tare da takin zamani. Mu a Arewa muna buƙatar waɗannan takin. Shin suna nufin za su dakatar da shi?” in ji shugaban APC.

Source: Twitter
Shawarar shugaban APC ga 'yan adawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bukaci shugabannin 'yan adawa su daina sukar gwamnati kawai.
Farfesa Nentawe ya bukaci su mayar da hankali wajen gabatar da ingantattun hanyoyin magance kalubalen tattalin arzikin Najeriya.
Asali: Legit.ng

