'Yan Daba Sun Sassara Matashi Mai Shayi da Wukake har Ya Mutu
- Rundunar ’yan sandan Adamawa ta fara bincike kan mutuwar Muhammad Auwal Idris, wani matashin mai sayar da shayi a Jimeta
- An ce matashin ya gamu da ajalinsa ne bayan wasu matasa huɗu sun kai masa hari a ranar Litinin, 28 ga Satumba, 2026
- Rundunar ta ce ta gano mutanen da ake zargi da hannu a lamarin, amma sun tsere kuma ana ci gaba da ƙoƙarin kamo su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Adamawa – Rundunar ’yan sandan jihar Adamawa ta fara cikakken bincike kan mutuwar wani matashin mai sayar da shayi daga Nassarawo Borehole, Jimeta, Muhammad Auwal Idris da ake zargin wasu matasa sun kai masa hari har ya mutu.
Rundunar ta ce ɗan uwan mamacin, Aliyu Idris, ne ya kai rahoton lamarin hedikwatar ’yan sanda ta Doubeli a ranar 28 ga Satumba, inda ya ce wasu mutane huɗu sun kai wa ƙaninsa hari.

Source: Facebook
Kakakin 'yan sandan jihar Adamawa, Suleiman Yahaya ne ya fitar da sanarwa game da halin da ake ciki a wani sako da ya wallafa a Facebook.
An kai matashin asibiti
Bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda sun gaggauta zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka tarar da Muhammad Auwal kwance ya suma.
Jami’an sun kwashe shi zuwa wani asibiti domin a ba shi kulawar gaggawa, amma likitan da ke aiki a asibitin ya tabbatar da cewa ya mutu bayan an kai shi.
Rundunar ta ce an kai shi dakin ajiye gawa domin gudanar da binciken gawar domin gano cikakken abin da ya haddasa mutuwarsa.
Mutanen da ake zargi
Binciken farko da ’yan sandan suka fara ya gano sunayen mutanen da ake zargi da hannu a lamarin, wadanda suka hada da Isa, Japhet, Omo da Henry.
Rundunar ta ce mutanen sun tsere, kuma jami’anta na ci gaba da ƙoƙarin gano inda suke domin kama su tare da gurfanar da su gaban kotu.
Kwamishinan ’yan sandan Adamawa, CP Kabir Umar Hassan, ya yi Allah-wadai da lamarin tare da umartar tawagar jami’ai ta ƙara kaimi wajen kamo waɗanda ake zargin.

Source: Original
Kiran 'yan sanda ga jama’a
Rundunar ta ce ta lura da rahotanni da damuwar da ake yadawa a kafafen sada zumunta kan lamarin, inda ta buƙaci jama’a su kwantar da hankula.
Ta kuma yi kira ga mazauna Nassarawo da yankin Banga da su guji ɗaukar doka a hannunsu, tare da bai wa ’yan sanda sahihan bayanai da za su taimaka wajen kama waɗanda ake zargi.
Rundunar ta tabbatar wa jama’a cewa za ta gudanar da bincike mai zurfi da ƙwarewa, sannan duk wanda aka samu da hannu a lamarin zai fuskanci hukunci.
An kashe matar aure a Gombe
A wani labarin, mun ruwaito cewa ’yan fashi da makami a Gombe sun kai hari tare da daba wa matar wani sufeto ɗan sanda, Aishatu Salisu, wuka har ta mutu yayin da suke ƙoƙarin kwace wayarta a gidanta da ke Wuro Shi'e.
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4:35 na asubahin ranar 26 ga Satumban 2026, lokacin da wasu da ake zargin maharan ne dauke da adduna da takubba suka kutsa gidan Inspector Salisu Waziri.
Kakakin ’yan sandan Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya ce maharan sun yi ƙoƙarin kwace wayar Aishatu, amma ta yi ihu, lamarin da ya sa ɗaya daga cikinsu ya daba mata wuka kafin su tsere suka bar wayar.
Asali: Legit.ng

