Bayan Nasarar Isa Ali Pantami, PDP Ta Kori Manyan Masu Masa Adawa 2 a Gombe
- Jam'iyyar PDP mai adawa reshen jihar Gombe ta dakatar da wasu jiga-jiganta biyu kwana ɗaya bayan nasarar Isa Ali Pantami
- Jam’iyyar ta ce wasu matakan mutanen biyu sun saɓa wa kundinta, musamman bayan wani daga ciki ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani
- PDP ta miƙa batun ga Kwamitin Ladabtarwa domin bincike da ɗaukar matakan da suka dace kan abubuwan da suka jawo dakatarwar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Pantami, Gombe - Jam’iyyar PDP ta reshen Jihar Gombe ta dakatar da Hon. Khamisu Ahmed Mailantarki da Hon. Usman Aliyu Garry.
Wannan mataki ya biyo bayan zarginsu da aikata abubuwan da suka saɓa wa manufofin jam’iyyar.
Hakan na cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar, Abdulkadir Ahmed Dukku ya fitar da aka wallafa a Facebook.
Matakin ya biyo bayan wani taron gaggawa da shugabannin PDP na jihar suka gudanar tare da shugabannin jam’iyyar na mazabun Dawaki da Herwagana, inda ’yan takarar biyu suke da alaƙa.
PDP ta ce duk da amincewar Mailantarki da Garry na shiga zaɓen fidda gwamnan jam’iyyar, wasu ayyukansu sun zama rashin da’a tare da karya tanadin kundin jam’iyya.
Shugabannin jam’iyyar sun nuna damuwa kan kalaman Mailantarki bayan zaɓen fidda gwani da aka gudanar ranar 29 ga Satumba, inda ya ce shi ne ya yi nasara.
A cewar PDP, irin waɗannan matakai na iya haifar da rashin fahimta da rarrabuwar kawuna tsakanin mambobinta, lamarin da ya sa aka ɗauki matakin dakatar da ’yan takarar.
Saboda haka, jam’iyyar ta dakatar da Mailantarki da Garry na tsawon wata guda tare da tura batunsu gaban Kwamitin Ladabtarwa domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakin da ya dace.
Sakataren Yaɗa Labarai na PDP a Gombe, AbdulKadir Ahmad Dukku, ne ya sanya hannu kan sanarwar da aka fitar a ranar 30 ga Satumba, 2026.
Karin bayani na tafe.....
Asali: Legit.ng
