Gobara Ta Tashi a Gidan Shugaban Karamar Hukuma a Kogi, Iyalansa na Ciki
- Gobara ta tashi a gidan shugaban karamar hukumar Ankpa da ke jihar Kogi, inda ta lalata kayayyaki masu yawa
- Shugaban karamar hukumar da iyalansa suna cikin gidan lokacin da mummunar gobarar ta tashi wadda ba a san musabbabinta ba
- Mazauna yankin sun kawo agaji inda suka taimaka wajen dakile gobarar domin kada ta bazu zuwa sauran gidaje makwabta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Ankpa, jihar Kogi – Wata gobara ta lakume gidan shugaban karamar hukumar Ankpa da ke jihar Kogi, Adamu Yahaya.
Gobarar ta lalata kayayyaki masu yawa da ke cikin gidan, ba tare da rasa ran mutum ko guda daya ba duk da barnar da ta yi.

Source: Original
Rahoton jaridar Daily Trust ya ce gobarar ta tashi ne ba zato ba tsammani da misalin karfe 11:00 na safe a ranar Laraba, 8 ga watan Yulin 2026 yayin da shugaban karamar hukumar da iyalansa suke cikin gidan.
Har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba, domin mazauna gidan da sauran mutanen da ke wurin sun ce lamarin ya faru ne cikin gaggawa kuma cikin yanayi mai cike da rudani.
An tabbatar da tashin gobarar
Babban sakataren yada labarai na shugaban karamar hukumar, Idris Mohammed Omale, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce shugaban karamar hukumar da iyalansa sun tsira daga gobarar, sai dai sun yi asarar kayayyaki masu yawa.
"Mun yi matukar kaduwa da wannan lamari da kuma asarar dukiyar da aka yi. Amma muna matukar godiya ga Allah da babu wanda ya rasa ransa."
"Duk da girman gobarar da ta tashi, an samu nasarar fitar da shugaban karamar hukumar da daukacin iyalansa cikin koshin lafiya ba tare da wani ya samu rauni ko rasa ransa ba."
- Idris Mohammed Omale
Mazauna yankin sun taimaka wajen kashe gobarar
Omale ya bayyana cewa gaggawar da mazauna unguwar, makwabta da sauran mutane suka yi wajen kai dauki ta taimaka matuka wajen hana gobarar bazuwa zuwa gidajen da ke makwabtaka.
Ya kuma gode wa al'ummar karamar hukumar da duk wadanda suka garzaya domin ba da taimako, yana mai cewa hadin kan da suka nuna da kokarin da suka yi a lokacin wannan iftila'i abin godiya ne kuma ba za a manta da shi ba.

Source: Twitter
Shaidu sun bayyana abin da suka gani
Wasu mazauna Ankpa sun ce hayakin da ya turnuke sararin samaniya tare da ihun mutane ne ya jawo hankalinsu zuwa wurin da gobarar ta tashi.
Sun ce da isarsu suka hada kai domin kokarin kashe gobarar tare da rage irin barnar da take yi.
Daya daga cikin mazauna yankin, Yusuf Obaje, ya ce:
"Gobarar ta lalata dukiya mai yawa da ke cikin gidan kafin yawancinmu mu isa wurin. Abin da ya sa muka ji sauki shi ne babu wanda ya rasa ransa. Dukiyar da gobara ta lalata za a iya maye gurbinta, amma rai ba za a iya ba."
Gobara ta lakume coci
A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin gobara a wata babbar coci da ke jihar Gombe a yankin Arewa maso Tsakiya na Najeriya.
Mummunar gobarar da ta tashe ne a cocin ECWA da ke kusa da hanyar Ashaka a birnin Gombe, inda ta kama rigi-rigi.
Hukumar kashe gobara ta yi kira ga al'umma da su dauki matakan kare kai daga gobara da kuma sanar da hukuma nan take idan an ga wuta ta kama wani wuri.
Asali: Legit.ng

