Amurka Ta Dauki Matsaya, Ta Sanar da Kasar Iran Shawarar da Ta Yanke kan Batun Sulhu

Amurka Ta Dauki Matsaya, Ta Sanar da Kasar Iran Shawarar da Ta Yanke kan Batun Sulhu

  • Kasar Musulunci ta Iran ta ce ta karɓi martanin Amurka kan shirin kawo ƙarshen yaƙin Gabas ta Tsakiya
  • Tehran ta gabatar da sharuɗɗa bakwai domin dakatar da yaƙi da sake buɗe mashigar ruwa ta Hormuz cikin kwanaki bakwai
  • Iran ta ce tana buƙatar tsagaita wuta a Gabas ta Tsakiya da ɗage takunkuman tattalin arziki da Amurka ta kakaba mata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Mahukuntan Iran sun ce sun karɓi martani a hukumance daga Amurka kan shawararta ta kawo ƙarshen yaƙin Gabas ta Tsakiya.

Wannan sakon amsa da Amurka ta mika wa Iran kan tayin tsagaita wuta na zuwa ne kwanaki bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da shirin.

Iran.
Shugaban kasar Musulunci ta Iran, Masoud Pezeshkian a bakin aiki Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Tashar Al-Jazeera ta ruwaito cewa Amurka ta gabatar da shawarar da ta yanke kan yiwuwar kawo karshen yaki ga shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian.

Kara karanta wannan

Iran ta bankado karairayin Trump, ta yi masa barazana a yankin Gabas ta Tsakiya

Amurka ta mika matsayarta ga Iran

Kakakin gwamnatin Iran, Fatemeh Mohajerani, ta tabbatar da hakan yayin hira da manema labarai, sai dai ba ta bayyana matsayar da Amurka ta dauka ba.

“Kamar yadda aka tattauna a taron yau, an gabatar da shawarar bangaren Amurka ga Shugaba Masoud Pezeshkian ta hannun Ministan Harkokin Waje Abbas Araghchi,” in ji ta.

Bayan watanni bakwai na rikici, Amurka da Iran sun sake komawa tattaunawar kai tsaye a makon da ya gabata a gefen taron Majalisar Ɗinkin Duniya.

Iran ta yi wa Amurka tayin sulhu

Iran ta ce ta gabatar da sharuɗɗa bakwai domin kawo ƙarshen fadan da kuma sake buɗe mashigar ruwan Hormuz, wadda ke da muhimmanci wajen jigilar man fetur da iskar gas zuwa kasuwannin duniya.

Mashigar Hormuz na tsakiyar rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran, wanda ya fara ne bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ƙarshen watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sake kunyata Donald Trump

Tehran ta sanya wa mashigar Hormuz takunkumi bayan fara yaƙin, lamarin da ya sa Washington ta mayar da martani da nata takunkumin kan tashoshin jiragen ruwa na Iran.

Sharuɗɗan da Iran ta gabatar

Ko da yake ba a bayyana dukkan sharuɗɗan ba, Iran na buƙatar tsagaita wuta a faɗin Gabas ta Tsakiya, ciki har da Lebanon, inda ƙungiyar Hezbollah da ke kawance da Iran ke fafatawa da sojojin Isra’ila.

Haka kuma, Iran na buƙatar a saki dukiyarta da aka rike ƙasashen waje, a ɗage takunkuman da aka kakaba wa ɓangaren man fetur ɗinta, tare da kawo ƙarshen takunkumin jiragen ruwan Amurka.

Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yana magana da yan jarida a fadar White House Hoto: Kevin Dietsch
Source: Getty Images

Trump ya yi watsi da shirin yayin da yake magana da manema labarai ranar Asabar, amma Tehran ta ci gaba da jiran martanin a hukumance ta hannun masu shiga tsakani daga Qatar.

Fadan ya ragu a ’yan makonnin nan, sai dai Tehran ta ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa da ke kokairn wuce wa ta mashigar Hormuz, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Shugaban Iran ya soki Amurka

Kun ji cewa shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya yi kakkausar magana a Majalisar Ɗinkin Duniya, yana mai cewa Iran ba za ta mika wuya ba.

Shugaba Pezeshkian ya zargi Amurka da sikata ta’addanci kan kisan tsohon Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, a farkon yaƙin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262