Ci Gaba da Tsare El Rufai: Jam'iyyar ADC Ta Fallasa Shirin Gwamnatin APC

Ci Gaba da Tsare El Rufai: Jam'iyyar ADC Ta Fallasa Shirin Gwamnatin APC

  • ADC ta zargi gwamnatin APC da kokarin tsare tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, har sai bayan zaben 2027
  • Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce jam'iyyar na ganin ana kakaba sharudan beli masu wahalar cikawa domin a ci gaba da tsare El-Rufai
  • Ya kuma yi ikirarin cewa idan wani abu ya faru da El-Rufai a tsare, shugaba Bola Tinubu ne zai dauki alhakin hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam'iyyar ADC ta zargi jam'iyyar APC mai mulki dangane da ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai.

Jam'iyyar ADC ta zargi APC da kitsa yadda za a ci gaba da tsare Malam Nasir El-Rufai, har sai bayan babban zaben shekarar 2027.

ADC ta yi fallasa kan APC
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rugai Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Sakataren yada labarai na kasa na ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da Channels TV a ranar Alhamis, 9 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

'Kar mu ji, kar mu gani': Atiku ya gargadi gwamnati game da Obi, El Rufa'i

Ya ce jam'iyyar ADC ba ta adawa da gurfanar da duk wanda ake zargi da laifi idan akwai hujjojin shari'a a kansa.

Sai dai ya ce ci gaba da tsare mutum kan laifuffukan da doka ta amince a ba da beli, tare da gindaya sharudan beli masu wahalar cikawa, na haifar da zargin cewa ana son ci gaba da tsare shi ne da gangan.

ADC ta bayyana shirin APC

"Abin da zan iya fada shi ne ra'ayin da ke cikin ADC shi ne gwamnatin APC ta yanke shawarar ba za ta saki Malam Nasir El-Rufai ba sai bayan zabe. Wannan shi ne abin da muka yi amanna da shi."
"Wannan shi ne shirinsu saboda sun san idan aka saki Malam Nasir El-Rufai, 'yan adawa za su kara karfi. Sun kuma san idan ya fito, zai tunasar da su wasu abubuwan da ba sa son a tuna."

- Bolaji Abdullahi.

Ya kara da cewa 'yan adawa na ganin ana yin duk mai yiwuwa domin El-Rufai ya ci gaba da zama a tsare har sai bayan zaben 2027.

Kara karanta wannan

'An ci fuskar doka: Hakeem Baba Ahmed ya soki gwamnati kan tsare El Rufa'i

ADC ta nuna damuwa kan lafiyar El-Rufai

Bolaji Abdullahi ya ce El-Rufai na fama da matsalar rashin lafiya, yana mai cewa iyalansa sun sanar da su cewa an kai shi asibitin lasa da ke Abuja kwanakin baya.

Kakakin na ADC ya ce likitoci sun ba da shawarar a ci gaba da sanya ido a kansa saboda lafiyarsa na tabarbarewa.:

"Mun fadi a fili, haka kuma Alhaji Atiku Abubakar, dan takararmu na shugaban kasa, ya fada cewa idan wani abu ya faru da Malam Nasir El-Rufai a tsare, Shugaba Bola Tinubu ne za a dora wa alhakin hakan domin shi ne shugaban kasa."
"Muna cewa akwai fursunan siyasa a Najeriya a yau, kuma sunansa Malam Nasir El-Rufai."

- Bolaji Abdullahi

ADC ta nuna damuwa kan lafiyar El-Rufai
Kakakin jam'iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi Hoto: @BolajiADC
Source: Facebook

ICPC ta cafke likitan El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaki da cin hanci ta ICPC ta cafke Farfesa Bello Abubakar wanda shi ne likitin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai.

Hakazalika, hukumar ICPC Nasir El-Rufai, da karya sharuddan ziyarar asibiti da kotu ta amince masa yayin da yake tsare​ a hannunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng