"Ba Zan Amince ba"; Wike Ya Gano Dalilin Rashin Farin Jininsa a wajen Ma'aikata
- Nyesom Wike ya ce rashin farin jininsa a wurin ma'aikatan gwamnati ya samo asali ne daga matakan da ya dauka na dakile almundahanar kudaden jama'a
- Ministan na Abuja ya ce ya daina amincewa da kashe makudan kudi wajen zuwa tarurruka kasashen waje
- Wike ya bayyana cewa ya sauya tsarin kasafin kudin FCT ta hanyar bai wa ayyukan raya kasa kaso 70 cikin 100
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana dalilin da ya sa ba ya samun farin jini a tsakanin ma'aikatan gwamnati.
Wike ya ce hakan ya samo asali ne daga matakan da ya dauka na rufe hanyoyin da ake amfani da su wajen karkatar da kudaden jama'a.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce ya bayyana hakan ne a yayin taron tattaunawarsa da manema labarai na wata-wata kan halin da kasa ke ciki, wanda aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, 9 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya ta yi wa sojoji ƙarin lbashi mai gwaɓi don inganta walwalarsu a Najeriya
Dalilin Wike na dakatar da tafiye-tafiye
Ministan ya ce kudaden da a baya ake kashewa wajen halartar tarurruka a kasashen waje yanzu an karkata su zuwa ayyukan raya kasa, musamman gina tituna.
Ya bayyana cewa ya ki amincewa da abin da ya kira kashe kudaden gwamnati yadda bai dace ba, inda ya fifita ayyukan da za su amfani mazauna FCT kai tsaye.
"Muna barnatar da dukiyarmu a kan abubuwan da ba su da amfani. Kuna so na amince da a kashe kudi domin ku je Amurka taro kan kula da harkokin filaye, wannan wace irin amfani ne? Ku je Legas da Fatakwal, ku duba yadda tsarin nasu yake aiki ko bai yi aiki ba, sannan ku kwatanta da namu."
- Nyesom Wike
Wike ba zai amince da kudin zuwa tarurruka ba
Wike ya ce babu dalilin amincewa da kashe makudan kudade domin halartar tarurruka a kasashen waje, yana mai cewa irin wadannan kudade sun fi dacewa da ayyukan raya kasa.
"Ta yaya za ku sanya na sanya hannu a kashe Naira miliyan 20 domin tafiya Amurka taron mako guda kan harkokin filaye? Ba zan yi hakan ba."
- Nyesom Wike
Yadda Wike ya sauya kasafin kudin FCT
Ministan ya bayyana cewa kafin ya karbi mukami, kusan kaso 65 cikin 100 na kasafin kudin FCT ana ware shi ne domin kashe-kashen yau da kullum, jaridar The Cable ta kawo labarin.
Sai dai ya ce ya sauya tsarin ta yadda kaso 70 cikin 100 na kasafin kudin yanzu ake warewa ayyukan raya kasa, yayin da kaso 30 cikin 100 kacal ake warewa kashe-kashen yau da kullum.

Source: Twitter
Dalilin da ya sa ma'aikata ba su son Wike
Wike ya yi zargin cewa wasu kudaden da ake warewa da sunan halartar tarurruka suna ba da damar karkatar da kudaden jama'a.
Ya ce ya zabi amfani da irin wadannan kudade wajen ayyukan da za su amfani al'ummar FCT.
"Shi ya sa ba zan taba zama mai farin jini a wajen ma'aikatan gwamnati ba. Idan ka tambayi kowa a yau, Ministan da ba za su so ba ni ne. Me ya sa? Saboda kudin da ake kashewa wajen tarurruka, na tattara su na mayar da su aikin gina tituna."
- Nyesom Wike
Tinubu ya yabawa Wike
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya yaba game da ayyukan alheri da Ministan Abuja, Nyesom Wike ke gudanarwa.
Tinubu ya yaba da aikin Wike ke yi yana cewa ya fahimci manufofi da hangen nesan gwamnatinsa, musamman Ajandar 'Renewed Hope'.
Asali: Legit.ng

