'Yan Najeriya Za Su Fada Tsananin Talauci da Karancin Abinci, IMF Ta Yi Bayani
- Asusun IMF ya tabbatar da hasashen bunkasar tattalin arzikin Najeriya zuwa kashi 4.1 cikin 100 a 2026 ba tare da yin wani sauyi ba
- Asusun ya yi gargadi cewa hauhawar farashin kayan masarufi za ta kara tsananta talauci da matsalar karancin abinci a Najeriya
- IMF ya bukaci Najeriya ta kara tara kudaden shiga, inganta kashe kudade da ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki masu dorewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya tabbatar da hasashensa cewa tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa da kashi 4.1 cikin 100 a shekarar 2026.
Sai dai kuma, IMF ya yi gargadi cewa hauhawar farashin kayayyakin masarufi za ta kara jefa mutane cikin tsananin talauci da karancin abinci.

Source: Facebook
IMF ya hango talauci a Najeriya
IMF ta bayyana hakan ne a sabon rahotonta na World Economic Outlook (WEO) na watan Yuli 2026 da aka fitar ranar Laraba, in ji rahoton The Cable.
Rahoton ya nuna cewa tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa da kashi 4.1 cikin 100 a bana, sannan ya karu zuwa kashi 4.3 cikin 100 a shekarar 2027, ba tare da wani sauyi daga hasashen da aka yi a watan Afrilu ba.
Asusun ya kuma ci gaba da hasashen cewa tattalin arzikin kasashen yankin Afrika da Sahara zai bunkasa da kashi 4.3 cikin 100 a 2026 da kuma kashi 4.5 cikin 100 a 2027.
IMF ta tabo batun tattalin arzikin Afrika
A cewar IMF, kyautatuwar daidaiton tattalin arziki da kuma sauyin kasuwancin duniya sun taimaka wa Najeriya, amma karin farashin kayan bukatun yau da kullum zai kara tsananta talauci da rashin wadataccen abinci.
Rahoton ya kara da cewa ci gaban tattalin arziki a kasashen Kudancin Afrika da Sahara zai bambanta daga kasa zuwa kasa, dangane da manufofin gwamnati, aiwatar da sauye-sauye da kuma yadda kasashen ke fuskantar kalubalen tattalin arzikin duniya.
IMF ta ce kasashen da ke shigo da man fetur kuma ba su dogara da albarkatun kasa ba za su fi fuskantar matsin lamba sakamakon tashin farashin makamashi da kayan abinci, kamar yadda rahoton Punch ya nuna.
A bangaren tattalin arzikin duniya, IMF ta rage hasashen bunkasar tattalin arzikin duniya zuwa kashi 3 cikin 100 a shekarar 2026 daga kashi 3.1 cikin 100 da ta yi hasashe a watan Afrilu.

Source: Getty Images
Shawarwari ga Najeriya da kasashen Afrika
Asusun ya bukaci kasashe su kara karfafa tattalin arzikinsu ta hanyar inganta tara haraji, amfani da kudaden gwamnati yadda ya kamata da kuma aiwatar da sauye-sauyen da za su bunkasa samar da ayyukan yi da ci gaban tattalin arziki.
Har ila yau, IMF ta shawarci kasashen da ke fitar da albarkatun kasa da su guji kashe kudade fiye da kima idan kudaden shiga suka karu, tare da daukar matakan da za su tabbatar da ci gaba mai dorewa.
Najeriya za ta karbo bashin IMF
A wani labari, mun ruwaito cewa, asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya yi tayin ba da bashi ga kasashen Afrika da rikicin yankin Gabas ta Tsakiya ya shafa.
Ministan kudi na Najeriya, Wale Edun, ya koka da cewa mafi yawan kasashen Afrika na fuskantar matsalar fadawa cikin mawuyacin hali kan bashi.
Wale Edun ya kuma bayyana matsayar Najeriya kan ko a halin yanzu tana da shirin tunkarar IMF domin sake neman bashi.
Asali: Legit.ng


