Daga Fara Kai Hari, Amurka Ta Yi Wa Sojojin Kasar Iran Mummunar Ɓarna

Daga Fara Kai Hari, Amurka Ta Yi Wa Sojojin Kasar Iran Mummunar Ɓarna

  • Rahotanni sun ce sojojin Iran takwas sun mutu a sababbin hare-haren da Amurka ta kai kudancin ƙasar musulunci ranar Laraba
  • Amurka dai ta sake kai hare-hare kasar Iran yayin da ake ci gaba da tattaunawa bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya
  • Gwamnatin Iran ta zargi Amurka da karya yarjejeniyar tsagaita wuta, kuma ta tabbatar da cewa a shirye take ta maida martani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Gwamnatin Iran ta tabbatar da cewa sojojin kasar takwas sun rasa rayukansu a sababbin hare-haren da Amurka ta kai Kudancin kasar.

A cewar rahoton, waɗanda suka mutu sun kasance jami'an rundunar sojin sama da ta ruwa ta Iran sakamakon hare-haren da Amukra ta kai jan biranen Bandar Abbas da Bushehr.

Hare hare.
Yadda ake harba makamai masu linzami a rikicin Gabas ta Tsakiya Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Iran ta yi barazanar mayar da martani

Tashar Al-Jazeera ta ce duk da cewa babu wata alama da ke nuna cewa Amurka za ta sake kai wani sabon hari nan take, manyan hafsoshin sojin Iran sun yi barazanar mayar da martani mai tsauri.

Kara karanta wannan

Yaki ya koma sabo: Iran ta jefa bama bamai kan sansanonin sojojin Amurka

Jami'an rundunar Khatam al-Anbiya sun bayyana cewa duk wani sabon hari daga Amurka zai fuskanci abin da suka kira "martani mai tsanani."

Iran ta zargi Amurka da karya yarjejeniya

Manyan jami'an gwamnatin Iran, ciki har da Ma'aikatar Harkokin Waje da Kakakin Majalisar Dokoki kuma babban mai shiga tsakani, Mohammad Bagher Ghalibaf, sun zargi Amurka da karya yarjejeniyar fahimtar juna (MoU).

Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran ta ce hare-haren sun karya sashe na 1 na yarjejeniyar da ya shafi tsagaita wuta da sashe na 5 wanda ya tanadi cewa Iran ce ke kula da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.

Haka zalika, Iran ta zargi Amurka da saba wa sashe na 10 wanda ya shafi sassaucin da aka yi wa fitar da man fetur na Iran.

Hormuz na da matuƙar muhimmanci ga Iran

Gwamnatin Iran ta jaddada cewa mashigar ruwa ta Hormuz na da matuƙar muhimmanci ga tattalin arziƙin ƙasar, kamar yadda Reuters ta kawo a rahoton da ta wallafa.

Ta bayyana cewa sama da kashi 90 cikin 100 na man fetur da sauran albarkatun makamashin kasar Iran na bi ta wannan hanya zuwa kasuwannin duniya.

Kara karanta wannan

Amurka ta kai hare hare Iran ana jana'izar Ali Khamenei

Ya zuwa yanzu, jami'an Iran sun yi kakkausar suka kan hare-haren, yayin da Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) ta sake jaddada aniyarta ta ɗaukar matakin ramuwar gayya.

A wani rahoton, kun ji cewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262