Lauya Ya Dauko da Zafi, Ya Maka Tinubu da Ministan Ayyuka Kara gaban Kotu

Lauya Ya Dauko da Zafi, Ya Maka Tinubu da Ministan Ayyuka Kara gaban Kotu

  • Wani lauya daga jihar Kogi ya maka Shugaba Bola Tinubu da wasu jami'ai ƙara kan zargin watsi da aikin hanyar Abaji zuwa Okene
  • Barrista Julius Elukpo ya ce ya nemi bayanai kan aikin hanyar ne ƙarƙashin dokar 'yancin samun bayanai (FOI) ta 2011 kafin ya garzaya kotu
  • Babbar kotun tarayya da ke Lokoja ta ɗage sauraron shari'ar zuwa ranar 22 ga wata mai zuwa domin ci gaba da shari'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Lokoja, Kogi - Wani ƙwararren lauya a jihar Kogi, Barrista Julius Elukpo, ya shigar da ƙara a babbar kotun tarayya da ke Lokoja a kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Ministan Ayyuka, Engr. David Umahi.

Karar da lauyan ya shigar ta kuma shafi wasu jami'ai biyu bisa zargin watsi da aikin hanyar Abaji-Koton Karfe-Lokoja-Okene.

Lauya ya kai karar Tinubu da Umahi
Ministan ayyuka, Dave Umahi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @daveumahi, @aonanuga1956
Source: Facebook

Jaridar Tribune ta ce sauran waɗanda ke cikin ƙarar sun haɗa da babban daraktan ma'aikatar ayyuka ta tarayya a jihar Kogi da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

'Kar mu ji, kar mu gani': Atiku ya gargadi gwamnati game da Obi, El Rufa'i

Lauya ya nemi bayanai kan aikin hanya

Barrista Elukpo ya bayyana cewa tun farko ya rubuta wa Ministan ayyuka wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 23 ga Maris, 2026, inda ya nemi bayani kan halin da aikin hanyar yake ciki bisa tanadin dokar Freedom of Information (FOI) Act, 2011.

A cikin wasiƙar, ya koka kan irin wahalar da direbobi da sauran masu amfani da hanyar ke fuskanta, yana mai cewa yanayin hanyar ya zama abin takaici.

Ya kuma buƙaci a bayyana sunayen kamfanonin da ke aikin, kuɗin kwangilar, adadin kuɗin da aka fitar a matsayin kuɗin fara aiki, yawan aikin da aka kammala, da kuma dalilan da suka sa aka yi watsi da aikin.

Kotu ta ɗage sauraron shari'ar

Bayan abin da ya bayyana a matsayin amsa mara gamsarwa, Barrista Elukpo ya nemi izinin babbar kotun tarayya domin fara shari'ar a kan waɗanda ake ƙara.

An fara sauraron shari'ar a gaban mai shari'a Isah Dashen na babbar kotun tarayya da ke Lokoja, wanda ya ɗage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 22 ga wata mai zuwa, rahoton shafin Kogireports ya tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan

Matar Tinubu za ta tara matan Kano ta ba su tallafin kayan sana'a

"Ba zan yi kasa a gwiwa ba"

Da yake zantawa da manema labarai bayan zaman kotun, Barrista Elukpo ya ce zai ci gaba da bin shari'ar har sai an kammala aikin hanyar.

"Ba zan yi kasa a gwiwa ba har sai an gyara wannan hanya. Mutane suna shafe kwanaki a kanta saboda mummunan yanayinta, kuma hakan ba abin da za a yarda da shi ba ne," in ji shi
Lauya ya kai karar Tinubu da Umahi
Taswirar jihar Kogi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Hanyar Abaji-Koton Karfe-Lokoja-Okene na daga cikin manyan hanyoyin gwamnatin tarayya da ke haɗa Abuja da jihar Kogi da kuma wasu sassan Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabashin Najeriya. Tsawon lokaci matafiya na ci gaba da nuna damuwa kan lalacewar hanyar.

Akpabio ya yi hasashe kan nasarar Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya yi magana kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Akpabio ya ce yana hasashen jam'iyyun adawa za su rika ikirarin cewa an tafka magudin zabe idan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sake samun nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng