Tambuwal Ya Fadi Dalilin 'Yan Siyasa Na Shiga ADC bayan Karbar Ciyaman da Ya Yi Murabus

Tambuwal Ya Fadi Dalilin 'Yan Siyasa Na Shiga ADC bayan Karbar Ciyaman da Ya Yi Murabus

  • Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya ce masu kishin jama'a da kaɗai za su iya shiga jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya
  • Tsohon gwamnan ya zargi APC da tsoratar da 'yan siyasar da ke son komawa ADC tare da ƙoƙarin haddasa rabuwar kai a jam'iyyar
  • Tambuwal ya kuma soki gwamnatin Tinubu kan matsalar tsaro, yana mai cewa rashin tsaro ya sa 'yan Najeriya da dama sun gaji da APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana irin 'yan siyasar da ke shiha jam'iyyar ADC.

Tambawul ya ce 'yan siyasar da ke da ƙarfin guiwa kuma suka himmatu wajen yi wa jama'a hidima maimakon neman amfanin kansu ne kaɗai za su iya shiga jam'iyyar ADC.

Tambuwal ya yi magana kan ADC
Sanata Aminu Waziri Tambuwal a zauren Majalisar Dattawa Hoto: Sen. Aminu Waziri Tambuwal
Source: Facebook

Tambuwal ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 8 ga watan Yulin 2026 yayin da yake karɓar tsohon shugaban ƙaramar hukumar Tangaza, Hon. Isa Salihu Kalenjeni, zuwa jam'iyyar ADC, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Mai martaba Sarkin Ilorin ya yi wa 'yan takarar APC addu'a ta musamman gabanin zaben 2027

Hon. Isa Salihu Kalenjani ya shiga ADC ne bayan ya yi murabus daga mukaminsa tare da ficewa daga jam'iyyar APC mai mulki.

Tambuwal ya yi kira ga 'yan siyasa

Sanatan ya ce duk wanda ya yi amanna cewa abin da yake yi saboda jama'a ne da kuma neman yardar Allah, ba don wata riba ta kansa ba, bai kamata ya ji tsoron bayyana kansa a matsayin ɗan ADC ba.

"Duk wanda ya yi amanna cewa abin da yake yi saboda jama'a ne da kuma neman yardar Allah, ba don amfanin kansa ba, ya kamata ya kasance da ƙarfin guiwar barin kowace jam'iyyar siyasa ya shiga ADC."

- Sanata Aminu Waziri Tambuwal

Ya zargi APC da tsoratar da masu sauya sheƙa

Tambuwal ya yi zargin cewa APC na tsoratar da 'yan siyasar da ke son sauya sheƙa zuwa ADC, tare da ƙoƙarin haddasa rashin haɗin kai a cikin jam'iyyar adawa.

A cewarsa, jam'iyya mai mulki yanzu tana kallon ADC a matsayin babbar ƙalubalen siyasa da take fuskanta.

Tambuwal ya zargi gwamnatin APC
Aminu Waziri Tambuwal na gaida tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo Hoto: Sen. Aminu Waziri Tambuwal
Source: Facebook

Ya soki gwamnati kan matsalar tsaro

Kara karanta wannan

2027: Malami ya gana da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a Abuja

Tambuwal ya kuma soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan halin rashin tsaro da ake ciki a ƙasar.

Ya ce 'yan Najeriya da dama sun fara gajiya da APC saboda ci gaba da matsalolin rashin tsaro wadanda suka ki ci suka ki cinyewa.

Sanatan ya yabawa Hon. Isa Salihu Kalenjeni bisa matakin da ya ɗauka na yin murabus daga mukaminsa tare da shiga ADC ba tare da gindaya wani sharadi ba.

Ya bayyana matakin a matsayin sadaukarwa da kuma nuna cikakken jajircewa ga manufofi da akidun jam'iyyar.

Tambuwal ya hakura da takara

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya janye daga takarar kujerar Sanatan Sokoto ta Kudu a majalisar dattawa.

Aminu Tambuwal wanda shi ne jagoran jam'iyyar a Sokoto ya hakura da takarar sanata a karkashin ADC mai adawa a Najeriya.

Tsohon gwamnan ya dauki matakin ne bayan tattaunawa da rashin jituwa kan zaben ‘yan takara gabanin babban zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng