Mbappe da Dembele Sun Rusa Burin Moroko, Faransa Ta Kai Wasan Kusa da na Ƙarshe

Mbappe da Dembele Sun Rusa Burin Moroko, Faransa Ta Kai Wasan Kusa da na Ƙarshe

  • Faransa ta doke Moroko da ci 2-0, inda Mbappe da Dembele suka zura ƙwallaye suka kai Les Bleus wasan kusa da na ƙarshe
  • Mbappe ya ci ƙwallo a minti na 60 bayan ya kasa cin bugun fenariti a farkon wasan, wanda ya fara sanya farin ciki a zukatan 'yan Faransa
  • Moroko ta kasa maimaita tarihin 2022 bayan ta sha kashi a hannun Faransa a gasar cin kofin duniya, inda a yanzu za ta koma gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka - Faransa mai rike da kambun zakarun duniya ta samu gurbin shiga wasan kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin duniya bayan ta doke Moroko da ci 2-0 a wasan da suka fafata a ranar 9 ga watan Yuli.

Kyaftin Faransa, Kylian Mbappe, ne ya fara jefa ƙwallo a ragar Moroko a filin wasa na Gillette Stadium da ke Foxborough, Massachusetts, a minti na 60, bayan da ya kasa cin bugun fenariti a farkon wasan.

Kara karanta wannan

Kotu ta ci tarar dan takarar gwamna a ADC miliyoyi kan fastocin siyasa a Adamawa

Faransa ta kai wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya bayan ta doke Morocco
Mbappe, Dembele da wasu 'yan wasan Faransa na murnar cin kwallo. Hoto: Jean Catuffe/Getty Images
Source: Getty Images

Mbappe da Dembele sun ciwa Faransa kwallo

Da wannan ƙwallon, Mbappe mai shekara 27 ya yi kunnen doki da kyaftin Argentina, Lionel Messi, a saman jerin ‘yan wasan da suka fi zura ƙwallaye a gasar, inda kowannensu ke da ƙwallaye takwas, in ji rahoton France 24.

Bayan mintuna shida kacal, Ousmane Dembele ya ƙara wa Faransa ƙwallo ta biyu bayan wani gagarumin gudu da ya yi, wanda ya tabbatar wa Les Bleus damar shiga wasan kusa da na ƙarshe, inda za su fafata da wanda ya yi nasara tsakanin Spain da Belgium.

Duk da cewa Faransa ta fi riƙe ƙwallo a wasan, ta sha fama wajen amfani da damar da ta samu a farkon fafatawar.

Bayan ya hana Mbappe cin fenariti mai sauƙi, mai tsaron ragar Moroko, Yassine Bounou, ya sake yin wani babban ceto inda ya hana Desire Doue zura ƙwallo, kafin Faransa ta kusa samun ƙarin ƙwallo a lokacin ƙarin lokaci, amma bugun Lucas Digne ya sauka kan sandar raga.

Kara karanta wannan

Farashin mai ya haura Dala 80 bayan Trump ya sake rura rikicin Iran

Rashin nasarar Moroko gasar Kofin Duniya

Sai dai Moroko ba ta samu damar matsa wa mai tsaron ragar Faransa, Mike Maignan, lamba sosai ba.

Tawagar Atlas Lions ta yi wasan ba tare da babban ɗan wasanta na gaba, Ismail Saibari, wanda ya samu rauni a wasan da ya gabata, lamarin da ya sa ta rasa ƙarfi a gaban ragarta.

Hakan ya sa Moroko ta kasa maimaita tarihin da ta kafa a gasar cin kofin duniya ta 2022, inda ta zama ƙasar Afirka ta farko da ta kai wasan kusa da na ƙarshe. A wancan lokacin ma Faransa ce ta doke ta da ci 2-0 a wannan matakin.

Idan Faransa ta samu nasara a wasan kusa da na ƙarshe da za ta buga ranar 14 ga watan Yuli, za ta zama ƙasa ta biyu a Turai da ta kai wasan ƙarshe na gasar cin kofin duniya sau uku a jere, bayan Jamus da ta yi hakan a shekarun 1982, 1986 da 1990.

Kara karanta wannan

Sanata ya zargi Ali Modu Sheriff da ƙoƙarin jefa ƙiyayya tsakanin Obi da ƴan Arewa

Shin akwai wanda zai iya dakatar da Faransa?

Kasancewar Faransa ba ta taɓa shiga baya da ci ba a wannan gasar na nuna irin ƙarfin da take da shi, a cewar wani rahoto na The New York Times.

Sai dai abin zai kasance mai ban sha’awa idan wata ƙungiya kamar Spain ta samu damar fara cin ƙwallo a wasan kusa da na ƙarshe, ko kuma Ingila ta yi hakan a wasan ƙarshe.

Faransa ta je wasan kusa da na karshe bayan doke Moroko
Mbappe ya rungume Demebele bayan ya ciwa Faransa kwallo a wasansu da Moroko. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Faransa ta fi haɗari ne musamman idan tana kan gaba da ci, domin hakan na tilasta wa abokan hamayya buɗe wasa domin neman ramawa, wanda ke ba ‘yan wasanta masu saurin gudu damar yin ƙarin barna.

A wasan da suka yi da Moroko, hakan ne ya faru bayan Mbappe ya buɗe ƙwallaye, inda Dembele ya jagoranci harin gaggawa da ya ƙare da ƙwallo ta biyu da ta tabbatar wa Faransa matsayinta a zagayen gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com