Cuta Ta Barke a Sansanin 'Yan Ta'addan ISWAP, Mayaka da Dama Sun Mutu
- Rahotanni sun nuna cewa barkewar cutar kwalara ta kashe mayaƙan kungiyar 'yan ta'addan ISWAP tara a dajin Timbuktu da ke jihar Borno
- Majiyoyin sirri sun bayyana cewa rashin magunguna da matsin lambar sojoji sun jefa sansanonin ƴan ta'addan cikin mawuyacin hali
- An kuma yi zargin cewa mayaƙa biyu da suka kamu da cutar sun rasa rayukansu bayan da takwarorinsu suka kashe su bayan an gaza ceto rayuwarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Wata barkewar cutar amai da gudawa (kwalara) ta yi sanadiyyar mutuwar mayaƙan Islamic State West Africa Province (ISWAP) tara a jihar Borno.
'Yan ta'addan na ISWAP dai sun mutu ne a yankin Timbuktu Triangle wanda aka fi sani da kasancewa sansanin ƴan ta'adda a jihar Borno.

Source: Original
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
Majiyoyin sirri sun bayyana cewa cutar ta bazu a sansanonin ƙungiyar, lamarin da ya nuna yadda yanayin tsafta ya tabarbare da kuma ƙarancin samun kulawar lafiya a wuraren da suke buya.
'Yan ISWAP sun kashe takwarorinsu
A cewar bayanan sirrin, wasu mayaƙan ISWAP biyu da suka kamu da cutar sun rasa ransu ne daga hannun takwarorinsu, inda suka harbe su bayan ƙoƙarin jinyarsu a ƙauyen Kimba ya ci tura.
Majiyoyin sun ce wannan al'amari ya ƙara nuna yadda matsalar lafiya ke ƙara ta'azzara a maboyar ƴan ta'addan, inda hare-haren da sojoji ke ci gaba da kai wa suka dagula hanyoyin samar da kayan aiki, ciki har da magunguna da damar samun kulawa ta lafiya.
Matsin lambar sojoji ya shafi ISWAP
Majiyoyin sun ƙara da cewa an buƙaci kwamandojin tsaro su ƙara ƙaimi wajen tare duk wani yunƙurin kai magunguna da kayan jinya zuwa sansanonin ƴan ta'addan domin ƙara raunana ƙarfinsu da kuma rage ƙarfinsu na ci gaba da kai hare-hare.
Rahoton barkewar cutar na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun Operation Hadin Kai ke ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin ƴan ta'adda da hanyoyin samar masu da kayan aiki a yankin Tafkin Chadi, da nufin rage ƙarfinsu na yaƙi.

Kara karanta wannan
Yadda sojoji suka fatattaki 'yan ta'adda da suka kai hari sansanin sojojin Zamfara
Dakarun sojoji dai sun dade suna gwabza fada da 'yan ta'adda a kokarin da suke yi na samar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas na Najeriya.

Source: Twitter
Mayakin ISWAP ya mika wuya ga sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa an yi kazamin dauki ba dadi tsakanin dakarun sojojin Najeriya da mayakan kungiyar 'yan ta'addan ISWAP.
Wani da ake zargin mayaƙin ISWAP ne, wanda aka horar da shi kan yakin tukin kwale-kwalen da kuma sarrafa babbar bindigar Dushka, ya miƙa wuya.
Binciken farko ya nuna cewa mutumin ya tsere daga sansanin 'yan ta'adda da ke ƙauyen Barra a yankin Tafkin Chadi kusa da Dogon Chukwu, wanda ake zargin yana ƙarƙashin jagorancin wani shugaban 'yan ta'adda mai suna Abu Ubeida.
Asali: Legit.ng
