Amurka Ta Sake Maganar Kare Kiristocin Najeriya, Ta Yi Gargadi kan Fulani

Amurka Ta Sake Maganar Kare Kiristocin Najeriya, Ta Yi Gargadi kan Fulani

  • Gwamnatin Amurka ta yaba da matakin da Najeriya ta ɗauka kan hare-haren baya-bayan nan da aka kai a yankin Arewa ta Tsakiya
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bukaci gwamnatin Najeriya ta ci gaba da ƙoƙarin kare al’ummomin Barkin Ladi da ke jihar Plateau
  • Wannan na zuwa ne yayin da yankin Barkin Ladi ke fama da hare-hare da ramuwar gayya, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin jama’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Plateau – Gwamnatin Amurka ta yaba da martanin da gwamnatin Najeriya ta mayar kan hare-haren baya-bayan nan a yankin Arewa ta Tsakiya, tare da kira ga hukumomin ƙasar su ci gaba da kare al’ummomin jihar Plateau.

Hakan na zuwa ne yayin da gwamnatin Najeriya ke cewa tana kara kokari wajen tabbatar da tsaro duk da matsalolin da ake kara fuskanta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar hutu saboda cikar Najeriya shekaru 66 da samun 'yanci

Shugaba Bola Tinubu da Donald Trump
Shugaba Bola Tinubu a hagu da Donald Trump a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: Facebook

Ofishin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka mai kula da harkokin Afirka ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata.

Maganar Amurka kan batun Barkin Ladi

Ofishin ya ce Amurka za ta ci gaba da aiki tare da gwamnatin Najeriya wajen kare Kiristoci a yankin Arewa ta Tsakiya.

Ta kuma bukaci Najeriya ta ci gaba da matakan da take ɗauka, musamman wajen kare al’ummomin Barkin Ladi.

Kalaman na zuwa ne yayin da wasu sassan yankin Arewa ta Tsakiya ke fuskantar hare-haren 'yan bindiga, satar mutane, rikicin al’umma da kuma rikicin manoma da makiyaya.

An kashe mutum 6 a Barikin Ladi

A ranar 27 ga Satumba, an kashe mutum shida tare da jikkata wasu biyu bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan wani wurin haƙar ma’adinai a ƙauyen Lajam Marit da ke gundumar Ropp, ƙaramar hukumar Barkin Ladi.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro da aka tura yankin sun gano gawarwakin mutanen shida da aka harbe, yayin da aka kai waɗanda suka jikkata asibiti domin samun kulawa.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta samar wa matasan Najeriya ayyuka a ƙasashen waje, an ji yadda tsarin yake

Kwana biyar kafin wannan hari, gwamnatin Plateau ta sanya dokar hana fita daga ƙarfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe a ƙananan hukumomin Barkin Ladi, Bokkos da Mangu sakamakon hare-hare da ramuwar gayya.

Taswirar jihar Filato
Taswirar jihar Filato a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

A ranar 20 ga Satumba, an ruwaito cewa an kashe aƙalla Fulani biyar bayan da wasu da ake zargin mayaƙan Berom ne suka kai hari kan motarsu a Barkin Ladi.

Rahotanni sun ce mutanen suna kan hanyarsu ta zuwa kasuwa a Jos South lokacin da aka kai wa motarsu hari kusa da wata cibiyar binciken jami’an tsaro.

An kara kai sojoji Zamfara

A wani labarin, mun ruwaito cewa Rundunar Sojin Najeriya ta kaddamar da sababbin bataliyoyin sojoji uku a jihar Zamfara domin ƙarfafa ayyukan tsaro da inganta saurin mayar da martani ga barazanar tsaro.

Sababbin bataliyoyin sun haɗa da 12 Infantry Battalion a Bakura, 23 Infantry Battalion a Kaura Namoda da 28 Infantry Battalion a Anka.

Kanar Joseph Umaru ya ce samun zaman lafiya mai ɗorewa na buƙatar haɗin gwiwar sojoji, sauran hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya da jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng