2027: Rarara Ya Sake Fitowa da Maganganu Masu Zafi kan 'Yan Arewa da Tinubu

2027: Rarara Ya Sake Fitowa da Maganganu Masu Zafi kan 'Yan Arewa da Tinubu

  • Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, ya sanar da cewa yana cigaba da alaƙa da jam’iyyar APC yayin da ake shirye-shiryen zabe
  • Rarara ya kuma yi ƙarin bayani kan kalamansa da suka jawo ce-ce-ku-ce, inda ya ce ’yan Kannywood da ke cikin ƙungiyarsa za su zaɓi Bola Tinubu
  • Ya ce yana da wasu bayanai da yake ganin za su sa ’yan Arewa su ci gaba da tallata Tinubu, yana mai cewa ƙungiyarsa na sauraron korafin talakawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, ya ce yana tare da jam’iyyar APC, yana mai bayyana irin gudunmawar da ya ce ya bayar wajen samun nasarar kafa gwamnatin jam’iyyar.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da caccaka tsinke tsakanin magoya bayan 'yan adawa da shugaban kasa mai ci, wato Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

'Za a yi babban haɗari idan Tinubu ya bari aka yi faretin 1 ga Oktoba,' Ayodele

Rarara tare da Bola Tinubu
Bola Tinubu tare da Aisha Humaira da Rarara. Hoto: Dauda Kahutu Rarara
Source: Twitter

Rarara ya bayyana hakan ne a wata hira da TRT Afrika ta wallafa a X, inda ya kuma yi ƙarin bayani kan matsayarsa game da goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Kiran Rarara ga 'yan Arewa

Mawakin ya bayyana cewa babu wanda zai nuna masu kishin Arewa a yanzu, saboda duk abin da ke faruwa suna da bayanai a kansu.

"Duk wani dan Arewa, indai ba ya so a yi wa 'ya'yan shi gori ya zabi Tinubu."

Rarara ya bayyana cewa za su fito da dalilai cewa dole ne 'yan Arewa su zabi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

A kan haka ya ce akwai wasu abubuwan da jama'a ba su sani ba a halin yanzu a kan zaben Bola Tinubu, ya ce da za a bayyana abubuwan mutane za su sha mamaki.

A kan tsaro kuwa, Rarara ya ce an samu sauyi, ya ce da ba ya bin hanyar Abuja amma yanzu da dare ma yana bi, inda ya ce:

Kara karanta wannan

Abba Kabir ya fada wa 'yan Arewa muhimmancin goyon bayan Tinubu

"Kokarin da ake yi ya fi na baya."

Alakar talakawa da Rarara

Rarara ya ce duk abin da suka samu suna ƙoƙarin rabawa jama’a, yana mai cewa hakan ya nuna muhimmanci magance matsalolin al'umma.

Ya ce talakawa suna gabatar musu da korafe-korafensu, sannan su kuma suka kai waɗannan korafe-korafe ga gwamnati domin a duba su.

Motocin tallata Tinubu
Lokacin da motocin tallata Tinubu da APC suka isa Nasarawa. Hoto: Gov Abdullahi A Sule Mandate
Source: Facebook

A cewarsa, sun rubuta korafe-korafe sama da 10 ga gwamnati kuma ana ba su amsa ɗaya bayan ɗaya, abin da ya ce yana daga cikin dalilan da suka sa suke ci gaba da goyon bayan Tinubu.

Tinubu cikin koshin lafiya

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo Najeriya bayan shafe makonni a kasashen Turai.

Shugaban kasar ya bayyanawa 'yan Najeriya cewa yana cikin koshin lafiya kuma zai cigaba da jan ragamar kasar ba tare da wata matsala ba.

Hakan na zuwa ne yayin da jama'a da dama ciki har da 'yan siyasa ke zargin cewa shugaban kasar ba shi da lafiya, yana asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng