Jirgin Sama Dauke da Mataimakiyar Shugaban Kasa da Wasu Mutum 8 Ya Yi Hatsari

Jirgin Sama Dauke da Mataimakiyar Shugaban Kasa da Wasu Mutum 8 Ya Yi Hatsari

  • Mataimakiyar shugaban kasar Zambia, Mutale Nalumango, ta tsira ba tare da rauni ba bayan jirgin mai saukar ungulu da take ciki ya fadi
  • An ruwaito cewa mutane takwas ne ke cikin jirgin lokacin da hatsarin ya faru yayin yakin neman zaben shugaban kasa da ke gudana
  • Nalumango ta ce ba a san musabbabin hatsarin ba, yayin da gwamnatin Zambia ta tabbatar tana cikin koshin lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zambia - Mataimakiyar shugaban kasar Zambia, Mutale Nalumango, ta tsallake rijiya da baya tare da wasu mutum bakwai bayan jirgin mai saukar ungulu da suke ciki ya yi hatsari.

Rahotanni daga Zambia sun nuna cewa cewa jirgin saman da ke dauke da mataimakiyar shugaban kasar ya yi hatsari ne jim kadan bayan tashinsa yayin yakin neman zaben kasar.

Kara karanta wannan

Wike ya tsage gaskiya kan yiwuwar PDP ta iya lashe zaben shugaban ƙasa a 2027

Mutale Nalumango.
Wurin da jirgin mataimakiyar shugaban Zambia, Mutale Nalumango ya fado kasa Hoto: Mutale Nalumango
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito vewa Zambia za ta gudanar da babban zaben shugaban kasa a ranar 13 ga watan Agustan 2026, inda ake sa ran Shugaba Hakainde Hichilema zai nemi wa'adi na biyu a mulki.

Yadda hatsrarin jirgin ya faru

Nalumango mai shekara 71 ta shaida wa manema labarai cewa hatsarin ya faru ne yayin da suke barin wani taron yakin neman zabe a garin Nakonde da ke Arewa maso Gabashin kasar.

Mataimakiyar shugaban kasar ta ce:

"Bayan jirgin ya tashi, ban san ko minti daya ko biyu ba, sai kawai muka dawo kasa. "Mutane takwas ne a cikin jirgin kuma dukkanninmu muna cikin koshin lafiya."

Mene ne ya haddasa hatsarin jirgin?

Mataimakiyar shugaban kasar ta bayyana cewa har yanzu ba a san abin da ya haddasa hatsarin ba, sai dai ta ce jirgin ya samu mummunar matsala sakamakon fadowar da ya yi.

Bayan hatsarin, Nalumango ta yi gwajin lafiya na gaggawa, inda gwamnatin Zambia ta tabbatar cewa an sallame ta daga asibiti cikin koshin lafiya, kamar yadda jaridar Malawi 24 ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a gidan shugaban karamar hukuma a Kogi, iyalansa na ciki

Jirgin.
Jirgi mai saukar angulu da ya yi hatsari bayan dauko mataimakiyar shugaban kasar Zambia Hoto: Echoes ZM
Source: Facebook

Hotuna sun nuna yadda jirgin ya lalace

Hotunan da aka wallafa a kafafen sada zumunta sun nuna jirgin mai saukar ungulu na rundunar sojin saman kasae Zambia a kwance gefe guda bayan da ake zargin ya bugi wata bishiya kafin ya rikito ƙasa.

Lamarin ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin yayin da yakin neman zaben shugaban kasa ke ci gaba a kasar, sai dai babu wanda ya rasa ransa ko ya samu munanan raunuka a hatsarin.

Jirgin sama ya yi hatsari a Faransa

A wani labarin na daban, kun ji cewa wani jirgin sama da ke amfani da shi wajen daukar masu koyon tsalle daga sama ya gamu da hatsari mai muni a gabashin kasar Faransa.

Kara karanta wannan

2027: Fadar shugaban kasa ta yi magana kan barazanar kashe Peter Obi

Mahukuntan yankin sun tabbatar da cewa mutane 11 ne suka mutu a hatsarin da ya faru a kusa da filin jirgin saman garin Tomblaine a ranar Lahadi, 28 ga watan Yuni, 2026.

Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Faransa ta tabbatar da cewa Ministan Harkokin Cikin Gida, Laurent Nunez, ya kai ziyara wurin da hatsarin ya faru domin duba hakikanin abin da ya auku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262