Yadda Shugaban Ma'aikatar Bogi Ya Yaudari Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai

Yadda Shugaban Ma'aikatar Bogi Ya Yaudari Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai

  • Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya ce ya gana da Adeniyi Adeyemi bayan ya karɓi wasiƙar da ta yi kama da ta fadar shugaban kasa
  • Benjamin Kalu ya ce ma'aikatansa sun tabbatar da akwai ofishin da aka rubuta a wasiƙar kafin ya amince da ganawar
  • Ya ce lamarin ya nuna akwai buƙatar ƙara tsaurara matakan tantance hukumomi masu ikirarin wakiltar gwamnatin tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja – Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya bayyana cewa ba tare da sani ba ya karɓi baƙuncin Adeniyi Adeyemi, wanda ya yi ikirarin shi ne shugaban hukumar PFIPC.

Benjamin Kalu ya ce ya karbi bakuncin Adeyemi ne bayan ya samu wata wasiƙa da ta yi kama da ta hukuma daga fadar shugaban kasa.

Adeyemi ya yaudari Benjamin Kalu
Adeniyi Adeyemi tare da mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu Hoto: Adeniyi Adeyemi Matthew
Source: Facebook

Kalu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin zaman majalisa na ranar Laraba, 8 ga watan Yulin 2026, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Ma'aikatar bogi: Yadda Adeniyi Adeyemi ya yi magana da Gbajabiamila

Ya yi magana ne lokacin da yake bayar da gudummawa kan ƙudirin da ke neman gudanar da cikakken bincike kan ayyukan hukumar, wadda daga baya fadar shugaban kasa ta musanta cewa tana da alaƙa da ita.

Yadda wasiƙar ta sa ya amince da ganawar

Da yake ba da labarin abin da ya faru, mataimakin shugaban majalisar ya ce ofishinsa ya karɓi wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 2 ga Mayu, 2025.

A cewarsa, wasiƙar ta gabatar da wanda ya turo ta a matsayin babban daraktan Presidential Economic Advisory Council da kuma PFIPC.

Kalu ya ce takardar ta yi kama da ta hukuma domin tana ɗauke da tambarin fadar shugaban kasa, adireshin ofishi a sakatariyar gwamnatin tarayya da ke Abuja, tare da shafin intanet na gwamnati mai suna pfipc.gov.ng.

Ya ce duk da cewa wasu bayanai sun sa ya fara shakku, salon da aka tsara wasiƙar ya sa ta yi kama da sahihiyar takardar gwamnati.

Benjamin Kalu ya ce saboda haka ne ya umarci ma'aikatansa su binciki hukumar kafin a amince da buƙatar ganawar.

Ma'aikata sun tabbatar da akwai ofishin

Kalu ya ce duk da shakkun da yake da su, ya umurci ma'aikatansa su je su tabbatar da sahihancin adireshin da aka rubuta, jaridar Tribune ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

An ji dalilan da suka jawo shugaban karamar hukuma ya yi murabus, ya bar APC a Sokoto

Mataimakin shugaban majalisar ya ce bayan sun je wurin, sun tabbatar cewa akwai ofishin a adireshin da ke cikin wasiƙar.

"Ko da yake ina da wasu shakku, na umarci ma'aikatana su tabbatar da ofishin kafin na amince da ganawar. Sun je wurin kuma suka tabbatar da cewa ofishin yana nan. Bisa wannan tabbaci ne na karɓe su."

- Benjamin Kalu

Ganawar ta sauya alkibla

A cewar mataimakin shugaban majalisar, tawagar ta nemi ganawa da shi ne da hujjar cewa tana son tattaunawa kan gyaran kundin tsarin mulki, tafiyar da tattalin arziki, manufofin majalisa da kuma zuba jari daga ƙasashen waje.

Sai dai ya ce bayan an fara zaman, tattaunawar ba ta mayar da hankali kan waɗannan batutuwa ba.

"Ba su yi magana kan kundin tsarin mulkin da muke gyarawa ba. Abin da ya fi damunsu shi ne ɗaukar hotuna."

- Benjamin Kalu

Benjamin Kalu ya ce Adeniyi ya yaudare shi
Benjamin Kalu yayin wani zama a zauren Majalisar Wakilai Hoto: House of Representatives Federal Republic of Nigeria
Source: Facebook

Kalu ya nemi a tsaurara matakan tantancewa

Benjamin Kalu ya ce abin da ya faru ya nuna akwai gibi a tsarin tantance ma'aikatu ko hukumomin da ke ikirarin wakiltar gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027: Jonathan ya wanke kansa kan zargin karɓo N500bn don raba ƙuri'ar Obi

Ya jaddada cewa bai kamata takardu masu kama da na hukuma, adireshin ofisoshi ko kuma shafukan intanet kaɗai su zama hujjar tabbatar da sahihancin kowace hukuma ba, domin dole ne a ƙara inganta hanyoyin tantancewa kafin a amince da irin waɗannan buƙatu.

Dalilin kafa hukumar PFIPC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Adeniyi Adeyemi da ke ikirarin shugabantar PFIPC, ya bayyana dalilin da ya sanya ya kafa hukumar.

Ya ce babban abin da ya ƙarfafa shi shi ne kishinsa ga Najeriya, burin jawo masu zuba jari daga ƙasashen waje da kuma tallata gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Adeniyi Adeyemi ya bayyana cewa bai kafa hukumar domin samun wani abu na kashin kansa ba sai don kishinsa ga kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng