Shugaban APC Ya Dawo daga Kasar Waje, Ya Fadi Abin da Za Su Yi wa Nyesom Wike
- Nentawe Yilwatda ya waiwayi rikicin kungiyar PGF da Nyesom Wike bayan dawowarsa daga gajeren hutu
- Shugaban APC na kasa yana kasar waje aka samu sabani tsakanin gwamnonin APC da Ministan Abuja
- Farfesa Yilwatda bai ga abin rigima ba, ya ce salin-alin za a shawo kan duk wani sabani a jam’iyyarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Shugaban APC na kasa baki daya, Nentawe Yilwatda ya yi zancen rigimar da ake yi da Nyesom Wike a jam’iyyarsa.
Farfesa Nentawe Yilwatda bai ganin sabanin Ministan harkokin Abuja da wasu shugabanni da manyan APC tamkar wani fada.

Source: Facebook
Nentawe Yilwatda ya shiga maganar Nyesom Wike
A farkon makon nan Leadership ta rahoto Nentawe Yilwatda yana mai cewa za a shawo kan lamarin ta hanyar lalama da dattaku.
Shugaban jam’iyyar a Najeriya ya ce burinsu shi ne tabbatar da hadin-kai da zaman lafiya da kuma hakkokin kowa gabanin zabe.

Kara karanta wannan
Akwai kura: Shugaban APC ya hango matsalar da Arewa za ta shiga idan Tinubu bai zarce ba
Game da batun Nyesom Wike wanda yake tare da ‘yan adawa duk da yana goyon bayan Bola Tinubu, ya ce za a mutunta juna.
Hadimin shugaban APC ya fitar da jawabi
Bayanin shugaban jam’iyyar na kasa ya fito ne ta bakin Mai taimaka masa wajen harkokin yada labarai da dabarun fitar da bayanai.
A jawabin da ya fitar a birnin Abuja, Abimbola Tooki ya ce samun sabani irin wannan a tsarin dimukaradiyya ba bakon abu ba ne.
A lokacin da Farfesa Yilwatda yake kasar waje, an samu baraka musamman tsakanin gwamnonin jihohin APC da Nyesom Wike.
An ji cewa sai kwanan nan ya dawo bayan shafe makonni biyu yana hutuwa a ketare.
Zaben 2027 jam'iyyar APC ta sa a gaba
Yilwatda ya ce sabani aka samu inda kowa yake da wata fahimta, kuma ya ce bai kamata a bari wannan ya kawar da hankali ba.
Tun da kowa ya bayyana matsayarsa, farfesan ya ce abin da ya kamata a tunkara shi ne zaben 2027.
A karshe Abimbola Tooki ya ce kofar shugaban na APC a bude ta ke kuma za su cigaba da karfafa jam’iyya donin cigaban kasa.

Kara karanta wannan
Matashin da ya yi rai ya bada labarin yadda mutane 37 suka mutu hannun NSCDC a Minna
Ya ce saboda haka, babu dalilin a yi ta kambama lamarin, za a shawo kan shi da tattaunawa, dattaku da girmama kowane bangarori.

Source: Facebook
Tafiya hutun shugaban jam'iyyar APC
A baya aka rahoto Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya fara hutun makonni biyu a ƙasashen waje bayan shekara a ofis.
Jam'iyyar ta bayyana cewa hutun zai ba shi damar samun nishadi da kuma sake tsara dabarun siyasa domin tunkarar babban zaɓe.
APC ta jaddada cewa rashinsa ba zai kawo cikas ga ayyukan jam'iyya ba, domin NWC zai ci gaba da tafiyar da komai bisa tsari a kasar.
Asali: Legit.ng