"Ba So Muke a Dakatar da Shari'a ba"; Bukatar Matar El Rufai ga Tinubu

"Ba So Muke a Dakatar da Shari'a ba"; Bukatar Matar El Rufai ga Tinubu

  • Matar Malam Nasir El-Rufai, Asiya El-Rufai, ta roƙi Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da kare haƙƙin mijinta na kundin tsarin mulki yayin da yake fuskantar shari'a
  • Ta ce ba sa neman a dakatar da shari'ar, sai dai a ba shi damar samun kulawar lafiya, lauyoyi, ziyarar iyali da beli bisa sharuɗɗa masu sauƙi
  • Asiya ta yi iƙirarin cewa akwai yiwuwar siyasa na taka rawa a yadda hukumomin da ke gabatar da ƙarar ke gudanar da lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCt, Abuja - Asiya El-Rufai, matar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ta roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Asiya ta roki Tinubu ya tabbatar da cewa ana kare haƙƙin mijinta na kundin tsarin mulkin Najeriya yayin da yake fuskantar shari'a.

Matar El-Rufai ta roki shugaba Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu da Mallam Nasir Ahmad El-Rufai Hoto: @aonanuga1956, @elrufai
Source: Facebook

Asiya, wadda lauya ce, ta bayyana hakan ne yayin wata hira da ta yi da Arise News a ranar Laraba, 8 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Ci gaba da tsare El Rufai: Jam'iyyar ADC ta fallasa shirin gwamnatin APC

Ta ce iyalansu ba sa neman shugaban ƙasa ya dakatar da shari'ar, amma suna roƙonsa ya tabbatar da cewa El-Rufai ya samu adalci kamar yadda doka ta tanada, ciki har da damar samun kulawar lafiya, lauyoyinsa, ziyarar iyalansa da kuma beli bisa sharuɗɗa masu sauƙin cikawa.

Asiya ta yi magana kan ci gaba da tsare El-Rufai

Roƙon nata na zuwa ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan tsare El-Rufai, da damuwar da ake nunawa kan lafiyarsa, da kuma kama likitansa na kashin kansa.

Ta kuma yi iƙirarin cewa ƙuntatawar da aka sanya masa na shafar yadda yake shirya kare kansa a gaban kotu.

Asiya ta ce laifuffukan da ake zargin mijinta da su laifuffuka ne da doka ta amince a ba da beli.

Sai dai ta koka da cewa duk lokacin da suka nemi beli, ko dai kotu ta ƙi amincewa ko kuma ta gindaya sharuɗɗan da ta ce suna da matuƙar wahalar cikawa.

Ta ce sharuɗɗan belin sun yi tsauri

"An gurfanar da Mallam a kotuna daban-daban kan wasu laifuffuka, kuma doka ta amince a ba da beli kan waɗannan laifuffuka. Ya nemi beli sau da dama. A babbar kotun jiha an ƙi ba shi beli. A babbar kotun tarayya an ba shi beli, amma bisa sharuɗɗan da ba su da sauƙin cikawa."

Kara karanta wannan

Kotu ta ci tarar dan takarar gwamna a ADC miliyoyi kan fastocin siyasa a Adamawa

- Asiya Nasir El-Rufai

Ta ƙara da cewa mai shari'a Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Kaduna ya ba El-Rufai beli ne da sharaɗin ya gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa, kowannensu da kadarar da ta kai darajar Naira miliyan 200 a GRA da ke Kaduna.

Wace bukata ta nema wajen Tinubu

A cewarta, kotun ta kuma buƙaci Majalisar Masarautar Kaduna ta bayar da takardar shaidar tabbatarwa, amma hakan ya gagara saboda majalisar ba ta ba su wannan takarda ba.

"Saboda haka muna roƙon shugaban ƙasa ne kawai ya tabbatar an bar doka ta yi aikinta. A ba shi damar fuskantar shari'a cikin adalci, kuma a bar kotuna su yanke hukunci."

- Asiya Nasir El-Rufai

An bukaci Tinubu ya sa baki kan shari'ar El-Rufai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai Hoto: Bello El-Rufai
Source: Facebook

ADC ta zargi APC kan tsare El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta zargi takwartarta ta APC kan ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai.

ADC ta zargi gwamnatin APC da shirya yadda za a ci gaba da tsare El-Rufai har sai bayan babban zaben shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng