Manyan Labarai A Yau
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa rashin tsaro na barazana ga gudanar da sahihin zabe.
Matatar Dangote da ke Legas ta sauya karin da ta yi a farashin da take sayar da litar man fetur ga 'yan kasuwa. Matatar ta ce farashin yana nan yadda yake.
Sanata Tony Nwoye ya raba gari da jam'iyyar ADC kwanaki kadan bayan komawa cikinta. Ya koma jam'iyyar NDC inda ya kafa hujja da rikicin cikin gida da ya addabi ADC.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi barazana ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Ya ce Amurka za ta kai hare-hare masu muni idan ba a cimma yarjejeniya ba.
An yi musayar yawu mai zafi tsakanin shugaban Majalisar dattawa, Godswill Akpabio da Sanata Adams Oshiomhole a zaman sanatoci, lamarin ya dauki lokaci.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya kalubalanci bangaren Tanimu Turaki, kan rikicin PDP. Ya yi barazanar kulle ofis idan suka bude shi.
Gwamnatin tarayya ta sanar da haramta wa masu digirin girmamawa amfani da Dr. a sunayensu, ta ce yadda ake ruwan karrama mutane da digirin ya fara wuce gona da iri.
Jam'iyyar ADC ta fitar da sabon jadawalin zaɓukan fitar da gwani na 2026, inda ta rage kudin fom ɗin takarar shugaban ƙasa zuwa N90m da na gwamna zuwa N30m.
Kamfanin sadarwa ta Airtel Nigeria ya cika umarnin hukumar NCC, ya fara turawa abokan cinikinsa katin waya a matsayin diyyar rashin karfin sabis da aka fuskanta.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari