Tofa: Kotu Ta Bada Umarnin Kwace Wasu Kadarorin Tsohon Ministan Najeriya, Sylva
- Kotu ta ba hukumar EFCC umarnin ƙwace wasu manyan kadarori guda tara da ke da alaƙa da tsohon ministan man fetur, Timipre Sylva
- Hukumar EFCC tana zargin cewa an mallaki waɗannan kadarorin ta hanyar sayensu da kudaden da aka samu ta haramtacciyar hanya
- Mai shari'a Obiora Egwuatu ya ɗage sauraron shari'ar zuwa 25 ga Mayu yayin da ake jira a ga ko wani zai yi adawa da wannan umarni na kotu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba gwanatin tarayya umarnin wucin gadi na ƙwace kadarori tara waɗanda ke da alaƙa da tsohon ministan man fetur, Timipre Sylva.
Mai shari'a Obiora Egwuatu ne ya bayar da wannan umarnin ne bayan lauyan hukumar EFCC, Oluwaleke Atolagbe, ya shigar da buƙatar hakan a gaban kotu.

Kara karanta wannan
Gwamnati za ta ba ma'aikata hutun kwanaki 9 domin bukukuwan sallar layya a Turkiyya

Source: Twitter
Kotu ta bada umarnin kwace kadarorin Timipre Sylva
Jaridar Daily Trust ta ruwaito alkalin ya na cewa:
“Wannan kotu mai daraja ta bada umarnin wucin gadi na ƙwace kadarorin da aka lissafa a cikin jadawalin da ke nan, waɗanda ake zargin an mallake su ta haramtattun hanyoyi, har sai an buga sanarwa da kuma sauraron ƙarar neman ƙwace kadarorin baki ɗaya. "
Mai shari'a Egwuatu ya kuma amince da buƙatar EFCC na wallafa wannan umarni a jaridun ƙasa cikin kwanaki bakwai.
Hukumar ta EFCC ta shigar da wannan ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/607/2026 a ƙarƙashin dokar 'aikata damfarar biyan kudi kafin aiki da sauran dangoginsu' ta shekarar 2006.
Jerin kadarorin Sylva da kotu ta kwace
Lauyan hukumar EFCC, Atolagbe, ya bayyana cewa ana zargin an mallaki kadarorin ne da kudin da aka same su ta haramtattun hanyoyi.
Kadarorin suna yankuna masu daraja a cikin birnin Abuja, waɗanda suka haɗa da manyan gine-gine da rukunin gidaje na alfarma.
Ga jerin wasu daga cikin kadarorin da abin ya shafa:
- Rukunin gidaje guda huɗu a yankin Dakibiyu.
- Gidan alfarma mai ɗauke da dakunan kwana da ofisoshi a titin Niger, Mpape.
- Gidan alfarma na kansa a Villa 1, Palm Springs Estate, Mpape.
- Rukunin gidajen sama mai gidaje 10 a Wuse Zone 4 da rukunin gidaje 6 a Garki.
- Manyan gidaje guda biyu masu ɗauke da bangarorin gidaje 12 a Thaba Tseka Crescent, Wuse II.
- Wani hamshaƙin gida a titin Nile Lake, Maitama, Abuja.
Kadarorin da NITDA take amfani da su
Kadara ta tara a cikin jerin kadarorin ita ce wasu gine-gine guda biyu waɗanda a halin yanzu Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA) take amfani da su a matsayin ofisoshi.

Source: UGC
Gine ginen suna nan a lamba ta 5, titin Aguta da ke yankin Garki a Abuja, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.
Alkali ya ɗage sauraron shari'ar zuwa ranar 25 ga watan Mayu domin karɓar rahoton yadda aka bi umarnin kotu.
Wannan matakin na kotu ya biyo bayan ƙwaƙƙwaran bincike da EFCC ke yi kan tsofaffin jami'an gwamnati da ake zargi da karkatar da dukiyar ƙasa.
Idan har babu wanda ya fito ya gabatar da kwararan hujjoji na dalilin da zai sa ba za a mallaka wa gwamnati kadarorin ba a cikin kwanaki 14, to kadarorin za su koma mallakar Gwamnatin Tarayya baki ɗaya.
EFCC ta kulle gidan Sylva, iyalansa na ciki
Tun da fari, mun ruwaito cewa, jami'an hukumar EFCC sun rufe gidan tsohon ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva da ke Abuja.
Mai magana da yawun tsohon ministan, Chief Julius Bokoru ya yi wa EFCC wankin babban bargo kan rufe gidan ubangidan nasa.
Chief Julius Bokoru ya yi ikirarin cewa an rufe gidan ne alhalin iyalin Sylva na rayuwa a ciki tare da iyalansa ba tare da hukumar ta ba su takarda ba.
Asali: Legit.ng

