Sabon Rikici Ya Barke a Garuruwan Jihar Kogi, An Rasa Rayukan Mutane Masu Yawa
- Wani sabon rikici da ya barke tsakanin garuruwan ƙaramar hukumar Ibaji, jihar Kogi ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da asarar dumbin dukiya
- Majiyoyi sun bayyana cewa wasu fusatattun mutane dauke da makamai sun kai hari a ranar Talata, don daukar fansar harin Nuwamban 2025
- Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da mutuwar mutum biyu kawai, amma wani mazaunin yankin da abin ya faru ya ce wadanda aka kashe suna da yawa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kogi - Sabon rikicin da ya barke tsakanin garuruwan Itale da Ishi a ƙaramar hukumar Ibaji ta jihar Kogi ya yi sanadin salwantar rayukan mutanen da ba a san adadinsu ba.
Baya ga kisan mutane, wannan sabon tashin hankalin, ya kuma jawo asarar dukiyar da ta kai ta miliyoyin naira, kamar yadda rahotanni suka nuna.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun nuna rashin imani, sun bude wa mutane wuta a wurin jana'iza a Filato

Source: Getty Images
Rikici ya barke a garuruwan jihar Kogi
Majiyoyi daga yankin a ranar Alhamis sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa wasu fusatattun mutane dauke da makamai suka far wa ƙauyen Ishi a ranar Talata a matsayin harin ramuwar gayya.
A lokacin harin, an bayyana cewa an kashe mazauna ƙauyen da dama, duk da cewa su ma sun dauki matakin kare kawunansu da ya jawo musayar wuta.
An kuma rahoto cewa maharan sun ƙone gidajen jama'a, kayan abinci da aka adana, da sauran kadarori masu daraja a cikin garin na Ishi.
An ce wadannan garuruwan da ke maƙwabtaka da juna sun daɗe suna takaddama kan filayen noma da rafunan kamun kifi, rikicin da aka gaza warware wa duk da ƙoƙarin zaman lafiya da aka yi ta yi tsawon shekaru.
Batu kan adadin mutanen da aka kashe
Mazauna garin Ishi sun zargi abokan hamayyarsu na Itale da shirya wannan harin tun bayan wani mummunan rikici da ya faru a ranar 9 ga Nuwamba, 2025, inda aka kashe mutane huɗu.
Wani mazaunin yankin, Omachonu Atule, da ya san yadda komai ya faru, ya bayyana cewa:
“Mutane masu yawa sun rasa rayukansu a wannan sabon harin. Har yanzu ba mu san adadin waɗanda aka kashe ba. Mutane da dama, ciki har da mata da yara, sun gudu zuwa ƙauyuka maƙwabta don neman mafaka.”
Sai dai, rundunar 'yan sandan jihar Kogi dai ta sanar da cewa an tsinci gawarwakin maza biyu a wurare daban-daban a cikin garin Ishi, in ji rahoton AIT.
Hakazalika an samu harsasan bindiga 57 yayin da aka kwantar da wani mutumi da ya samu raunukan harbin bindiga a asibitin Idah.

Source: Original
Matakin da 'yan sanda suka dauka
Kwamishinan ƴan sandan jihar, Naziru Kankarofi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa ofishin ƴan sanda na Ibaji ya karɓi kiran gaggawa a ranar 6 ga Mayu, 2026.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Saliu Oyiza Afusat ta sanya wa hannu, an tura tawagar haɗin gwiwa da ta haɗa da ƴan sanda, sojojin ruwa, da 'yan banga zuwa yankin.
Rundunar ta bayyana sunayen wasu mutane da ake nema ruwa a jallo daga ɓangarorin biyu, waɗanda suka haɗa da Stephen Enema, Isaac Enedubi, Alex Attah, da Eneje Idah daga Itale, da kuma Stephen Amegwu, Shederach Alone, da Friday Onal daga Ishi.
Yadda rayuka ke salwanta a rikicin filaye
A wani labari, mun ruwaito cewa, an gano yadda rikici a kan filaye da iyakokin kasa ke haddasa asarar rayuka da dama a sassan Najeriya daban-daban.
Bincike da wata kungiya ta PIND ta wallafa ya nuna yadda aka salwantar da rayuka akalla 1,796 daga watan 2018 zuwa 2025.
Rahoton ya nuna yankunan Kudu da Arewa ta Tsakiya sun fi fuskantar tasirin wannan tashin hankali a kan matsalar fili.
Asali: Legit.ng

