"Zai Fi na Baya"; Donald Trump Ya Sake Yin Babbar Barazana ga Iran
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sake yin barazana ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya dakatar da aikin 'Project Freedom' na yi wa jiragen ruwa rakiya
- Donald Trump ya gargadi Iran kan ta amince da yarjejeniyar kawo karshen yakin da ake yi wanda aka fara a watan Fabrairun 2026
- Shugaban na Amurka ya yi barazanar cewa abubuwa ba za su yi wa Iran kyau ba, idan har ta kuskura ta ki amincewa da yarjejeniyar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sake yin barazana ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Trump ya gargadi Iran cewa ko dai ta yarda da yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin ko kuma ta fuskanci sababbin hare-haren bama-bamai na Amurka masu tsanani.

Source: Getty Images
Trump ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Laraba, 6 ga watan Mayun 2026.
Wace barazana Donald Trump ya yi wa Iran?
“Idan har Iran ta amince ta ba da abin da aka amince da shi, wanda hakan babban zato ne, to tabbas aikin nan na ‘Epic Fury’ mai tasiri zai zo ƙarshe."
"Idan ba su amince ba, to za a fara kai hare-haren bama-bamai, kuma abin takaici, zai kasance a kan wani mataki da tsanani wanda ya ninka na baya.”
- Donald Trump
Jaridar Vanguard ta ce saƙon na Trump ya zo ne bayan an ruwaito cewa Washington da Tehran sun kusa cimma yarjejeniya kan wata wasiƙa ta shafi guda ɗaya don kawo ƙarshen yaƙin da kuma kafa tsarin tattaunawar nukiliya dalla-dalla.
Trump ya dakatar da yi wa jirage rakiya
A daren Talata ne Trump ya sanar da dakatar da aikin sojin Amurka na yi wa jiragen kasuwanci jagora ta mashigar Hormuz, bayan kwana ɗaya kawai da fara aikin, inda ya bayyana samun damar kulla yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin a matsayin dalili.

Source: Facebook
Shugaban na Amurka ya ce killace tashoshin jiragen ruwa na Iran da Washington ke yi zai ci gaba da kasancewa muddin Tehran ta ci gaba da rufe muhimmiyar hanyar kasuwancin, wanda hakan ya girgiza kasuwanni tare da haifar da tashin farashin man fetur.
Trump ya bayyana cewa shawarar dakatar da abin da ya kira “Project Freedom” kwana ɗaya bayan an fara shi, ta zo ne bayan buƙatun da mai shiga tsakani Pakistan da sauran ƙasashe suka yi, yana mai cewa an samu gagarumin ci gaba wajen cimma cikakkiyar yarjejeniya ta ƙarshe da Tehran.
Amurka ta nemi taimakon kasashe kan Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa Amurka ta nemi agajin kasashen duniya da su amince da kudirin da ta gabatar a gaban majalisar dinkin duniya.
Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya sanar da cewa lokaci ya yi da kasashen duniya za su amince a dauki mataki kan toshe Hormuz da Iran ta yi.
Marco Rubio ya bayyana cewa kudurin da Amurka ta gabatar zai gwada ko Majalisar Ɗinkin Duniya na da tasiri, inda ya yi kira ga China da Rasha kada su sake hana shi wucewa.
Asali: Legit.ng

