Dangote na Shirin Zuba Jarin da Zai Iya Share Hawayen 'Yan Najeriya a Harkar Wutar Lantarki
- Shugaban rukunin kanfanonin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote ya shiga zuba jari mai girma a fannin samar da wutar lantarki
- Hamshakin attajirin, wanda ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka ya ce kamfaninsa zai samar da wutar da ta kai megawatt 20,000
- A halin yanzu, Najeriya na samar da kusan megawatt 4,000 zuwa 4,500 na wutar lantarki, adadin da ya yi ƙasa sosai da adadin da ake bukata
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Aliko Dangote, attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, ya bayyana cewa rukunin kamfaninsa na Dangote Group na shirin zuba jari a harkar samar da wutar lantarki.
Dangote ya bayyana hakan ne a wata hira da shugaban Kamfanin International Finance Corporation (IFC), Makhtar Diop, a ranar Laraba.

Source: Getty Images
Aliko Dangote zai shigar harkar wutar lantarki

Kara karanta wannan
Alkawarin da sabon ministan makamashi ya dauka kan faduwar turakun wutar lantarki
Jaridar The Cable ta ruwiato cewa Dangote na shirin samar da megawatt 20,000 na wutar lantarki, wanda ake ganin zai yaye duk wata matsalar karancin wuta a Najeriya.
“Yanzu muna shirin shiga harkar wutar lantarki, megawatt 20,000," in ji shi.
A halin yanzu, Najeriya na samar da kusan megawatt 4,000 zuwa 4,500 na wutar lantarki, adadin da ya yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da ƙarfin da ƙasar ke da shi na sama da megawatt 13,000.
Dangote ya kuma lissafo wasu manyan ayyukan da kamfaninsa ke yi, ciki har da samar da takin zamani, iskar gas (LNG), da gina tashar jirgin ruwa mai zurfi, cewar rahoton Arise TV.
Dangote ya tuno da aikin matatar mai
Ya kuma yi magana kan yadda aka fara aikin matatar man Dangote, inda ya ce mutane da dama sun nuna shakku game da yiwuwar nasarar aikin a lokacin da aka fara shi.
“A lokacin da na fara wannan matatar mai, ban taɓa ganin ɗanyen mai da idona ba. Mutane sun rika yadawa a fili cewa wannan matatar ba za ta yi nasara ba," in ji shi.
Matatar man Dangote da aka kashe kusan Dala biliyan 20 wajen ginawa yanzu haka na samar da mai, tare da ƙarfin tace ganga 650,000 a rana.

Source: Getty Images
Dalilin Dangote na zuba jari a Afirka
Dangote ya ce wannan kalubale da ya fuskanta kafin nasarar aikin matatar, ya ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen saka hannun jari a manyan ayyuka a nahiyar Afirka.
“Ta yaya za mu bunƙasa Afirka? Za mu bunƙasa Afirka ne ta hanyar nuna cewa mun yi imani da Afirka, ta hanyar saka kuɗinmu a Afirka."
“Domin idan ban saka kuɗina ba, ba zan iya zuwa wani taro in shawo kan mutane cewa Afirka wuri ne mai kyau don zuba jari ba. Amma yanzu ina da bakin magana, na nuna cewa waɗannan abubuwa suna yiwuwa.”
- Aliko Dangote.
Ministan lantarki ya dauki alkawurra
A wani labarin, kun ji cewa sabon ministan lantarki da aka naɗa, Joseph Tegbe, ya yi alƙawarin magance yawan faɗuwar turakun wutar lantarki a Najeriya.
Tegbe ya bayyana hakan ne ranar Laraba 6 ga watan Mayu 2926 yayin da yake amsa tambayoyin sanatoci a zauren majalisar dattawa a lokacin tantance shi.
Tegbe ya ce gwamnati za ta kuma ci gaba da rabon mitocin wuta domin rage yawan korafe-korafen da suka shafi caji kudin da ya wuce misali.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
