Rigima Ta Kaure tsakanin Akpabio da Sanata Oshiomhole a Zaman Majalisar Dattawa

Rigima Ta Kaure tsakanin Akpabio da Sanata Oshiomhole a Zaman Majalisar Dattawa

  • Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya yi musayar yawu mai zafi da Sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole
  • Lamarin ya faru ne lokacin da Akpabio ke karanto bayanan zaman Majalisa na ranar Talata, wanda sanatoci suka gyara dokar neman shugabanci
  • Sanata Oshimhole ya yi kokarin yin magana amma shugaban Majalisar ya hana shi, lamarin da ya jawo musayar yawu na akalla mintuna 15

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja – Rikici ya kaure tsakanin shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da Sanata Adams Oshiomhole a zaman Majalisa na yau Laraba a Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa Sanata Akpabio da Oshiomhole, tsohon shugaban APC na kasa sun yi cacar baki mai zafi har tsawon mintuna 15, lamarin da ya kawo rikici a zaman.

Akpabio.
Shugaban Majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio yayin da yake jagorantar zaman sanatoci a Abuja Hoto: @Akpabio
Source: Facebook

Yadda rikicin ya faru a Majalisar dattawa

Kara karanta wannan

Pantami ya yi martani da APC ta yi amfani da tsarin 'sulhu' a tsayar da ɗan takara

Vanguard ta ruwaito cewa rikicin ya fara ne yayin da Akpabio ke karanta bayanan zaman ranar Talata, inda Oshiomhole ya yi kokarin magana, amma shugaban majalisar ya hana shi.

Sanata Akpabio ya dakatar da Oshiomhole, yana mai cewa dokokin majalisa ba su ba da damar hakan a wannan lokaci ba.

Duk da gargadin, Oshiomhole ya ci gaba da magana, lamarin da ya sa aka kira tsohon mai tsawatarwa, Sanata Orji Kalu, domin ya yi bayani kan dokar, inda shi ma ya goyi bayan Akpabio.

Haka kuma babban mai tsawatarwa na bangaren masu rinjaye, Sanata Tahir Monguno, ya gargadi Oshiomhole cewa zai yi amfani da ikon da yake da shi idan bai dakata ba.

Duk da haka, Sanata Oshiomhole ya ci gaba da dagewa kan cewa dole ne a bi dokoki yadda ya kamata, kamar yadda tashar Channels tv ta kawo.

Godswill Akpabio ya gargadi Sanata Oshiomhole

A yayin zaman, Akpabio ya yi kakkausar gargadi ga Oshiomhole, yana mai cewa:

“Idan ka ci gaba da rashin da’a, za mu yi amfani da dokokin majalisa mu fitar da kai.”

Daga bisani, an kammala zaman tare da amincewa da bayanan zaman, bayan Sanata Adamu Aliero ya gabatar da kudiri, wanda Sanata Abba Moro ya mara masa baya.

Kara karanta wannan

Atiku ya ce zubar da jinin 'yan Najeriya zai kawo karshen Tinubu a 2027

Me ake ganin ya jawo rigima a majalisar?

Rikicin na da alaka da sabon gyaran dokokin majalisar dattawa da aka yi a ranar Talata, wanda ya takaita damar ‘yan majalisa masu shiga takarar kujeru daban-daban na shugabancin majalisa.

Dokar ta tanadi cewa sai sanatan da ya yi akalla wa’adi biyu a jere ne zai iya neman shugabanci a majalisar dattawa.

Majalisar dattawa.
Zauren Majalisar dattawa yayin da sanatoci ke tsakiyar zama a Abuja Hoto: Senate Nigeria
Source: Facebook

Wannan na nufin cewa sababbin ‘yan majalisa a majalisar tarayya ta 11 da za a zaba a 2027 ba za su iya tsayawa takarar shugabanci ba, sai dai wadanda suka taba zama a majalisa ta 9 da ta 10.

An ce wannan mataki an dauke shi ne domin tabbatar da bin tsarin gogewa da kuma kare martabar majalisa.

Oshiomhole ya nemi a soke lasisin MTN

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Adams Oshiomhole ya yi kira ga Gwamnatin Bola Tinubu da ta soke lasisin kamfanonin Afirka ta Kudu, musamman MTN da DSTV.

Kara karanta wannan

"Zan fito kamfe," Tinubu ya gano abin da 'makiyansa' ke shirin yakarsa da shi a zaben 2027

A yayin zaman majalisar dattawa na jiya Talata, Oshiomhole ya bayyana cewa lokacin zubar da hawaye da jaje ya ƙare, inda ya buƙaci a ɗauki matakin tattalin arziki mai zafi.

A cewarsa, soke waɗannan lasisin zai buɗe wa kamfanonin gida na Najeriya dama su mamaye waɗannan guraben aikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262