Bayan Ficewar Kwankwaso da Obi, ADC Ta Fitar da Sabon Tsarin Zaben 'Yan Takara

Bayan Ficewar Kwankwaso da Obi, ADC Ta Fitar da Sabon Tsarin Zaben 'Yan Takara

  • Jam'iyyar ADC ta fitar da sabon jadawalin ayyukan zaɓukan fitar da gwani na shekarar 2026, inda ta bayyana ranakun sayar da fom da na zabe
  • Sanarwar ta nuna cewa jam'iyyar ta sauya farashin fom ɗin takarar shugaban ƙasa, gwamnoni, da na 'yan majalisar tarayya da jihohi
  • Duk da haka, jam'iyyar ta ci gaba da bayar da rangwamen kashi 50 ga matasa, da kuma rangwamen kashi 25 ga mata da masu bukata ta musamman

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Jam'iyyar ADC ta fitar da jadawalin da ta sabunta na shirye-shirye da kuma ranakun zaben fitar da gwani da za ta gudanar a 2026.

Sabon jadawalin zaben fitar da gwanin na hade da jerin kudin sayen fom din takara, wanda aka rage sakamakon tattaunawar masu ruwa da tsaki da 'yan takara.

Kara karanta wannan

Bayan shigar Kwankwaso da Obi, NDC ta fadi 'yan takarar da za ta tsaida a 2027

Jam'iyyar ADC ta fitar da sabon jadawalin zabukan fitar da gwani na 2026
David Mark, shugaban jam'iyyar ADC na kasa. Hoto: @BolajiADC
Source: Twitter

Mai magana da yawun jam'iyyar na kasa, Bolaji Abdullahi ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a shafinsa na X a yammacin ranar Talata, 5 ga Mayun 2026.

Sabon jadawalin zaben fitar da gwanin ADC

A cikin sanarwar, jam'iyyar ADC ta bayyana cewa za ta fara sayar da fom din takara ne daga 1 ga Mayu, 2026, yayin da za a kammala sayar da fom din zuwa 6 ga Mayun, 2026.

Sanarwar ta kuma jaddada cewa 13 ga watan Mayu ce ranar karshe da 'yan takara za su mayar da fom din nuna sha'awar takararsu bayan sun kammala cika wa.

Kakakin jam'iyyar, ya bayyana cewa za a tantance masu neman takara a ranaku 14 da 15 ga watan Mayu, sannan a fitar da sakamakon tantancewar a ranar 17 ga Mayu.

Ranakun gudanar da zaɓukan fitar da gwani

Bayan kammala sauraron korafe-korafe tsakanin 18 zuwa 19 ga Mayu, 2026, jam'iyyar ADC za ta wallafa jerin sunayen waɗanda suka cancanta a ranar 20 ga Mayu, 2026.

Kara karanta wannan

ADC ta fadi hanyar da za ta zabi dan takarar shugaban kasa bayan ficewar Kwankwaso da Obi

Jadawalin ya nuna cewa za a gudanar da zaɓukan fitar da gwani na ƴan majalisun jihohi da na tarayya (wakilai da dattawa) a ranar 21 ga Mayu, 2026.

A ranar 22 ga watan Mayu ne za a yi zaɓen fitar da gwani na gwamnoni, yayin da za a gudanar da na shugaban ƙasa a ranar 23 ga Mayu, 2026.

Daga nan kuma, jam'iyyar za ta gudanar da taron majalisar gudanarwa ta ƙasa (NEC) a ranar 25 ga watan, sannan ta kammala da babban taron ƙasa na musamman a ranar 26 ga watan Mayu, 2026.

Jam'iyyar ADC ta fitar da sabon jadawalin zabukan fitar da gwani.
Rotimi Amaechi, Rauf Aregbesola, David Mark a taron jam'iyyar ADC a Abuja. Hoto: @BolajiADC
Source: Twitter

Farashin fom da rangwamen da aka yi

Bayan nazarin da jam'iyyar ta yi, an tsayar da sabon farashin fom ɗin neman takara kamar haka:

  • Shugaban kasa: N90,000,000
  • Gwamna: N30,000,000
  • Sanata: N10,000,000
  • Majalisar wakilai: N5,000,000
  • Majalisar jiha: N2,000,000

Jam'iyyar ta nanata cewa tana nan kan matsayinta na bayar da rangwamen kashi 50 ga matasa masu shekaru tsakanin 18 zuwa 35. Haka kuma, mata da mutane masu bukata ta musamman za su samu rangwamen kashi 25 na kuɗin fom ɗin.

Karanta sanarwar a nan kasa:

Kara karanta wannan

NDC ta buɗewa Obi ƙofa, ta mika tikitin takarar shugaban ƙasa ga Kudancin Najeriya

Kwankwaso, Obi sun bar ADC zuwa NDC

A wani labari, mun ruwaito cewa, Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, sun sauya sheka daga ADC zuwa jam’iyyar NDC a hukumance.

Sun yi kira ga mambobin jam’iyyar da su guji yawan shari’o’in kotu, su mayar da hankali kan ci gaban ƙasa da kuma haɗin kan al’ummar Najeriya.

A bikin shigarsu NDC, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso sun aika muhimmin sako ga magoya bayansu yayin ake tunkarar babban zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com