NDC Ta Kara Karfi a Majalisa, Sanatan ADC Ya Sauya Sheka zuwa Cikinta
- Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta sake gamuwa da koma baya bayan daya daga cikin sanatocin da take da su ya fice daga cikinta
- Sanata Tony Nwoye mai wakiltar Anambra ta Arewa ya sanar da sauya shekarsa zuwa jam'iyyar NDC bayan raba gari da ADC
- Tony ya kafa hujja da kararrakin da ake yi kan ADC a kotu a matsayin dalilinsa na raba gari da jam'iyyar wadda bai dade ba a cikinta
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar mazaɓar Anambra ta Arewa, Tony Nwoye, ya yi murabus daga jam’iyyar ADC mai adawa a Najeriya.
Sanata Tony Nwoye ya sanar da sauya sheka zuwa NDC, wanda hakan ya sanya shi zama sanata na uku da ya shiga jam’iyyar a cikin mako guda.

Source: Facebook
Sanata Tony Nwoye ya koma jam'iyyar NDC
Jaridar TheCable ta ce Sanata Tony Nwoye ya sanar da sauya sheƙar tasa ne a cikin wata wasiƙa da Godswill Akpabio ya karanta a lokacin zaman majalisar dattawa na ranar Laraba, 6 ga watan Mayun 2026.
“Na rubutu muku wasikar ne domin sanar da ku murabus ɗina daga jam’iyyar ADC, da kuma nufina na komawa jam’iyyar NDC."
- Tony Nwoye
Meyasa ya fice daga ADC?
Ɗan majalisar ya danganta matakin nasa da rikicin cikin gida da kuma shari’u da dama da ake ci gaba da yi a babbar kotun tarayya, jaridar Daily Trustsha ta kawo rahoton.
Ya ƙara da cewa hukuncin kotu na baya-bayan nan kan ADC ya shafi haɗaka da kuma zaman lafiyar jam’iyyar.
Sanata Nwoye ya ce hakan ya raunana tsarin haɗakar da ke cikin jam’iyyar, sannan ya sa ya yi wahala ADC ta kasance cikin haɗin kai da gudanar da ayyukanta.
Wasu sanatoci sun koma NDC
Sauya sheƙar tasa na zuwa ne kwana ɗaya bayan da Victor Umeh, sanatan Anambra ta Tsakiya, ya bar ADC ya koma NDC, inda ya bayyana rarrabuwar kai da shari’u da ke cikin jam’iyyar a matsayin dalilinsa.

Kara karanta wannan
NDC: Kwankwaso ya mika sakon kar ta kwana gabanin rufe rajistar jam'iyyu a Najeriya
Rufai Hanga, sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, shi ma kwanan nan ya shiga NDC daga jam’iyyar NNPP, inda ya ɗora alhakin hakan a kan rikicin cikin gida da rigingimun ɓangaranci.

Source: Facebook
Waɗannan sauye-sauyen sheƙar na baya-bayan nan sun ƙara yawan mambobin NDC a majalisar dattawa zuwa mutum uku.
Bayan waɗannan sauye-sauyen, tsarin jam’iyyu a majalisar dattawa yanzu haka yana matsayin: APC tana da mambobi 87, ADC tana da bakwai, PDP tana da huɗu, NDC tana da huɗu, APGA tana da ɗaya, Accord tana da ɗaya, sannan LP tana da ɗaya.
A halin yanzu, jam’iyyar NNPP ba ta da ko sanata ɗaya a majalisar dattawa.
Sanata ya hakura da takara a 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanatan da ke wakiltar Yobe ta Gabas a Majalisar dattawa, Mustapha Musa, ya sanar da janyewarsa daga takarar zaɓen 2027 da ke tafe.
Sanata Mustapha Musa ya dauki wannan mataki ne domin ba Gwamna Mai Mala Buni dama tare da bayyana goyon bayansa domin ya nemi kujerar.
Mustapha Musa, wanda aka fi sani da Kulas, ya ce ba zai nemi wata kujera ta siyasa ba bayan janyewarsa daga fafatawar neman tikitin takara.
Asali: Legit.ng
