"Ba a Fahimce Ni ba," Ganduje Ya Bayyana Dalilin Kiran Sanusi II a Matsayin Sarkin Kano
- Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya ce an masa gurguwar fahimta a maganar da ya yi game da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II
- Ganduje ya ce a yanzu, ba shi da ikon amincewa ko kin aminta da wani a matsayin Sarkin Kano, yana mai cewa komai na hannun Kotun Koli
- Ya ce an fassara kalamansa ba daidai ba, yana mai cewa ya ambaci Sanusi da lakabinsa na sarauta a wurin rantsar da mataimakin gwamna don girmamawa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa Kotun Koli ta Najeriya ce kadai ke da ikon yanke hukunci kan rikicin sarautar Kano.
Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano, ya ce hukuncin da Kotun Koli za ta yanke shi ne za a aiwatar, kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf zai mutunta shi bisa tsarin doka.

Source: Facebook
Daily Trust ta ce Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da yake martani kan rahotannin da ke cewa ya amince da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano kuma Shugaban Majalisar Sarakuna.
Ganduje ya amince da Sarki Sanusi II?
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da tsohon kwamishinan yada labarai kuma shugaban ma’aikatansa, Kwamared Muhammad Garba, ya sanya wa hannu.
Ganduje ya ce an fassara kalamansa ba daidai ba, yana mai cewa ya ambaci Sanusi da lakabinsa na sarauta a wurin rantsar da mataimakin gwamna ne don girmamawa da bin ka’ida.
“Yana da muhimmanci mu fayyace cewa abin da ya faru shi ne nuna girmamawa a taron jama’a. Bai kamata a dauke shi a matsayin amincewa ba,” in ji shi.
Matsayar Ganduje kan sarautar Kano
Ya jaddada cewa rikicin sarautar na gaban kotu, yana gargadin cewa ya kamata a yi taka-tsantsan wajen yin tsokaci domin kaucewa saba wa kotu.

Kara karanta wannan
Iran ta yi magana, da yiwuwar yaki ya kuma barkewa tsakanin kasar Musulunci da Amurka
Tsohon gwamnan ya tuna cewa Kotun Daukaka Kara ta riga ta umurci bangarorin da su ci gaba da zama yadda suke har sai an yanke hukunci na karshe, cewar rahoton Leadership.
“A yanzu mun amince da Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano na 15, yayin da Muhammadu Sanusi II yake matsayin Sarkin Kano na 14, har zuwa lokacin da Kotun Koli za ta yanke hukunci na karshe,” in ji shi.

Source: Twitter
Ya kara da cewa a matsayinsa na tsohon gwamna, ba shi da ikon doka na amincewa ko kin amincewa da wani a matsayin sarki, yana mai cewa al’amarin gaba daya yana hannun bangaren shari’a da kuma Gwamna Abba.
“Fassarar da aka yi wa wannan magana ba daidai ba ne, don haka muna kira ga jama'a su jira hukuncin Kotun Koli wanda ake sa ran za a yanke a watan Afrilu na shekara mai zuwa,” in ji shi.
Sanusi zai yi bikin nadin sarauta
A wani rahoton, kun ji cewa masarautar Kano karkashin Mai martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II za ta yi biki nadin sarauta ga wasu hakimai da aka karawa matsayi.

Kara karanta wannan
Dalilin da ya sa Kotun Koli ta dage shari'ar rikicin sarautar Kano zuwa bayan zaben 2027
Rahotanni sun nuna cewa mai martaba Muhammadu Sanusi II ne ya amince da sauye-sauye da suka shafi wasu masu rike da sarauta.
A wata sanarwa da Danmakwayon Kano, Alhaji Abba Yusuf ya fitar, ya ce Hakiman Mariri da Garko na cikin wadanda za a yi wa karin girma a sarauta.
Asali: Legit.ng
