Bayan Abin da Ya Faru, An Haramta wa Masu Digirin Girmamawa Amfani da 'Dr' a Najeriya

Bayan Abin da Ya Faru, An Haramta wa Masu Digirin Girmamawa Amfani da 'Dr' a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta hana masu digirin girmamawa amfani da Dr a jikin sunayensu bayan gano cewa ana karya ka'ida a tsarin
  • Ministan ilimi na tarayya, Dr. Tunji Alausa ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da manema labarai a fadar shugaban kasa yau Laraba
  • Alausa ya ce duk jami’ar da ta saba wa wannan umarni za ta fuskanci hukunci, yana mai cewa an umurci shugabannin jami’o’i su daidaita tsarin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta dauki matakin banbanta digirin PhD na girmamawa da wadanda suka zauna a aji.

Gwamnatin ta sanar da cewa daga yanzu, ta haramta wa masu wannan digiri da girmamawa amfani da 'Dr.' a farkon sunayensu.

Tunji Alausa.
Ministan ilimi, Dr. Tunji Alausa yana jawabi a wurin taro a Abuja Hoto: @DrTunjiAlausa
Source: Twitter

Ministan Ilimi na tarayyar Najeirya, Dr. Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Laraba, 6 ga watan Mayu, 2026, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wasa farin girki: Minista ya cike takardar takarar Tinubu a 2027

Dalilin hana amfani da Dr a farko suna

Tunji Alausa ya ce an dauki matakin ne a taron majalisar zartarwa ta kasa (FEC) da aka yi a makon da ya gabata, watau ranar 30 ga Afrilun 2026.

Ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne domin kawo karshen yadda ake bayar da digirin girmamawa ba bisa ka’ida ba, musamman don siyasa da neman kudi.

A baya-bayan na dai an ba da irin wannan digiri ga shahararren mawakin siyasra nan, Dauda Kahutu Rarara, wanda hakan ya haifar da ce-ce-ku-ce kan zargin inganacin karramawar.

Gwamnatin tarayya ta gano kuskure

Da yake jawabi ga manema labarai a Aso Villa, Ministan Ilimi ya ce:

“Abin da muke gani a baya-bayan nan na bayar da digirin girmamawa ya nuna ana cin zarafin wannan mataki na ilimi.
"Ana amfani da shi wajen siyasa da kuma anfani na kudi, har ma ana bai wa masu rike da mukaman gwamnati, wanda bai dace ba.”

Kara karanta wannan

Matar da APC ta tsaida takara a Katsina ta fara fuskantar cikas daga malaman Musulunci

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana rattaba hannu kan kudirin doka a Aso Rock, Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Gwamnati ta gargadi jami’o’i game da rabon Dr

Ministan ya ce duk jami’ar da ta saba wa wannan umarni za ta fuskanci hukunci, yana mai cewa an umurci shugabannin jami’o’i su daidaita tsarin bayar da digirin bisa yadda doka ta tanada.

Ya kara da cewa daga yanzu, dole ne jami’o’i su nemi amincewar Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) kafin su bayar da irin wadannan digiri, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Najeriya za ta ci gaba da cin bashi?

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ba zai daina karbo wa Najeriya bashin kudi ba matukar akwai bukatar hakan.

Wannan bayani na zuwa ne a lokacin da ake kara nuna damuwa kan yadda bashin Najeriya ke karuwa da kuma yadda ake kashe kaso mai yawa na kudaden shiga wajen biyan bashin.

Tinubu ya ce maimakon sukar ciyo bashin da ake yi, kamata ya yi Najeriya ta dage wajen ganin ta biya basussukan da ke kanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262