Matatar Dangote Ta Sauya Farashin Fetur bayan Yin Karin N75 kan Kowace Lita
- A ranar Laraba, 6 ga watan Mayun 2026 an samu rahotannin da ke cewa matatar Dangote ta kara farashin litar fetur zuwa N1,350
- Wani jami'in matatar wanda ya tabbatar da karin da aka yi, ya kuma bayyana cewa an sauya farashin zuwa yadda yake a baya
- Sai dai, kuma matatar a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta bayyana cewa farashin da take sayar da litar fetur yana nan yadda yake
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Matatar Man Dangote ta janye ƙarin farashin fetur da ta yi a baya, inda ta mayar da farashin kowace lita na fetur zuwa N1,275.
Sauya farashin na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan sanar da dillalan mai sabon farashi ga 'yan kasuwa.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce wannan janyewar ta zo ne bayan da matatar man, a farkon ranar Laraba, 6 ga watan Mayun 2026 ta aiwatar da ƙarin farashi zuwa N1,350 kan kowace lita.
An sauya farashin fetur a matatar Dangote
Wani babban jami’i a matatar man Dangote, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da ƙarin farashin na farko amma ya ce matatar yanzu ta janye shi.
Ya bayyana cewa an ɗauki wannan shawarar cikin sauri ne sakamakon sauye-sauyen yanayin kasuwa, musamman faɗuwar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.
“An janye ƙarin farashin da aka yi a baya. Mun mayar da farashin lita zuwa N1,275,” inji jami’in.
Farashin danyen mai ya sauka
Bayanai sun nuna cewa farashin ɗanyen mai ya faɗi ƙasa sosai a safiyar ranar Laraba, inda ɗanyen mai na Brent ya faɗi zuwa dala $101.7 kan kowace ganga.
An yi cinikin danyen mai na West Texas a kan dala $94.11 kan kowace ganga, wanda ke hakan ke nina raguwar kashi 7.48 cikin 100 da kashi 7.98 cikin ɗari bi da bi.
To sai dai, duk da raguwar farashin, binciken da aka gudanar ya nuna cewa gidajen mai da dama sun riga sun ƙara farashin sayarwa ga jama’a zuwa har N1,400 kan kowace lita a Legas.

Kara karanta wannan
Bayan abin da ya faru, an haramta wa masu digirin girmamawa amfani da 'Dr' a Najeriya

Source: Facebook
Matatar Dangote ta ce ba ta yi kari ba
Jaridar The Cable ta kawo rahoton cewa matatar Dangote ta bayyana cewa farashin da take sayar da mai yana nan yadda yake.
A cikin wata sanarwa, matatar Dangote ta bayyana cewa ba ta sauya farashin ba, bayan wasu rahotanni sun nuna cewa an kara shi zuwa N1,350 kan kowace lita.
A cikin watan da ya gabata, Matatar Dangote ta sauya farashin fetur ɗinta sau da dama, sakamakon sauyin kuɗin sayo ɗanyen mai, matsin lamba na farashin canjin kuɗaɗen ƙasashen waje, da kuma yanayin rarraba man a cikin ƙasa.
Matatar Dangote ta hako danyen mai
A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar Dangote da ke Legas ta fara hako danyen mai a yankin Niger Delta na Najeriya.
Mataimakin shugaban matatar Dangote, Edwin Devakumar ya ce sun fara gwajin farko kan danyen mai daga kadarorin da yake da su a yankin Neja Delta.
Edwin ya ce kamfanin ya bude rijiyar mai guda da ya mallaka, inda aka fara gwajin da aka saba yi domin tantance ingancinsa.
Asali: Legit.ng
