Kamfanin Airtel Ya Bi Sahun MTN, Ya Fara Tura wa Mutane Kudi a Wayoyinsu a Najeriya

Kamfanin Airtel Ya Bi Sahun MTN, Ya Fara Tura wa Mutane Kudi a Wayoyinsu a Najeriya

  • Kamfanin Airtel ya fara raba wa mutane katin waya a matsayin diyyar tangardar sabis da aka fuskanta tsakanin watan Nuwamba, 2025 zuwa Janairu, 2026
  • Wannan mataki na zuwa ne bayan hukumar NCC ta umarci kamfanonin su biya abokan huldarsu diyyar rashin ingancin Intanet
  • Tuni dai kamfanin MTN ya tura wa mutane katin waya zuwa cikin layukansu, yayin da Airtel ya biyo bayansa a 'yan kwanakin nan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Kamfanin sadarwa na Airtel Nigeria ya fara biyan 'yan Najeriya diyyar matsalar sabis da suka fuskanta a tsakanin watan Nuwamba, 2025 zuwa Janairu, 2026.

Hakan na zuwa ne bayan hukumar sadarwa ta kasa (NCC) ta umarci kamfanonin sadarwa a Najeriya sun fara bai wa masu amfani da layukansu diyya sakamakon matsalolin sadarwa.

Kara karanta wannan

Kashe ministan taron Mali ya rikita Najeriya, ta kawo mafita kan ta'addanci

Ofis.
Daya daga cikin ofisoshin da kamfanin Airtel ke hulda da abokan cinikinsa a Najeriya Hoto: Airtel Nigeria
Source: Instagram

Kamfanin Airtel ya bi umarnin NCC

Jaridar Leadership ta tattaro cewa kamfanin Airtel ya fara bin wannan umarni na hukumar NCC duk da cewa har yanzu miliyoyin mutane na fama da matsalolin intanet da kira a kasar nan

Wannan mataki na zuwa ne a matsayin wani sabon yunƙuri na gwamnatin Najeriya na gyara fannin sadarwa da aka dade ana suka saboda matsalolin yankewar kira, jinkirin intanet da rashin ingancin sabis.

Bincike ya nuna cewa manyan kamfanoni kamar Airtel da MTN Nigeria sun fara tura wa abokan huldarsu katin waya ta layukansu a matssyin diyyar matsalolin sabis da aka fudkanta tsakanin Nuwamba 2025 da Janairu 2026.

An kuma bukaci masu amfani da Airtel da su duba asusun layinsu ta wasu lambobin USSD, yayin da masu amfani da MTN suka tabbatar da karbar sakonnin biyansu diyya.

Adadin katin da Airtel ke turawa

Duk da haka, an gano cewa kudin diyya da kamfanonin ke tura wa mutane bai da yawa, inda wasu ke ganin an ba su N20 zuwa N600, gwargwadon girman matsalar da aka fuskanta a yanki.

Kara karanta wannan

Amnesty ta ce Fulani 150 sun mutu a Kwara bayan sun sha azaba

Hukumar NCC ta bayyana cewa ba mayar wa mutane da kudindu aka yi ba, illa dai diyya ce da aka tanada saboda kamfanonin sun kasa cika ka’idojin ingancin sabis, cewar rahoton The Cable.

Dalilin NCC na daukar mataki

Shugaban hukumar NCC, Aminu Maida, ya ce matakin wani bangare ne na kokarin kare hakkin masu amfani da layukan sadarwa da kuma tilasta bin ka’idoji ga kamfanonin sadarwa.

Duk da wannan mataki, masana sun ce hakan bai warware matsalolin ba, kamar karancin kayan more rayuwa, tsadar aiki da kuma karuwar bukatar intanet.

Hukumar NCC.
Babbar hedkwatar hukumar NCC da ke birnin tarayya Abuja Hoto: NCC Nigeria
Source: Twitter

Wani masani kan harkar fasahar sadarwa, Teju Abolade, ya ce ba tare da karin zuba jari da inganta sabis ba, wannan diyya ba zai zama mafita mai dorewa ba.

Ya kara da cewa inganta sadarwa na da matukar muhimmanci ga hada-hadar kudi, kasuwancin yanar gizo da bunkasar tattalin arzikin zamani a Najeriya.

MTN ya biya yan Najeriya diyya

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin MTN ya rabawa mutane katin waya a layukansu domin biyan diyyar matsalar sabis da aka samu a watan Janairu, 2026.

Masu amfani da layukan MTN a Najeriya da dama sun tabbatar da cewa sun samu sakon katin waya a wayoyinsu,

Masu amfani da layukan MTN sun tabbatar da cewa kudin da aka tura ya bambanta, ba adadi daya aka tura wa kowa ba, inda aka tura wa wasu katin N20, wasu N91, yayin da wasu kuma suka samu har N341.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262