Pantamiyya Ta Yi Rashi, Hadimin Pantami Ya Bar Layinsa, Ya Koma Goyon bayan Jamilu Gwamna
- Tafiyar Farfesa Isa Ali Pantami ta neman gwamnan Gombe ƙarƙashin PDP ta gamu da cikas, bayan hadiminsa Muhammadu Buhari Dalhatu ya koma APC
- Buhari Dalhatu ya ce zai goyi bayan Sardauna Gombe, Dr Jamilu Isiyaku Gwamna, bayan nazari da la’akari da akidarsa da burinsa na siyasa
- Tsohon na kusa da Pantami ya ce zai ci gaba da kasancewa kusa da al’umma, tare da bayar da gudunmawa wajen ci gaban Gombe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Pantami, Gombe - Tafiyar Farfesa Isa Ali Pantami da ke neman gwamnan jihar Gombe ƙarƙashin PDP ta ci karo da babban cikas.
Daga daga cikin na kusa da shi kuma hadiminsa a bangaren matasa da alumma ya koma jam'iyyar APC mai mulkin jihar.

Source: Facebook
Hon Muhammadu Buhari Dalhatu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Asabar 8 ga watan Agustan 2026.
Na hannun daman Pantami ya watsar da tafiyarsa
Buhari ya kasance na kusa da Farfesa Pantami shekara da shekaru kafin raba alaka da shi a yanzu ana daf da fara kamfe na zaben gwamnoni.
A cikin wata sanarwa, ya ce daga yanzu zai goyi bayan tare da aiki da Sardauna Gombe, Dr Jamilu Isiyaku Gwamna, a tafiyar siyasarsa.
Ya bayyana cewa ya yanke wannan shawarar ne bayan yin dogon nazari, tare da la’akari da akidarsa, burinsa na siyasa da kuma sha’awar kasancewa kusa da al’umma.
Ya ce yana son ci gaba da kasancewa da alaka da jama’ar kasa, tare da bayar da gudunmawa mai ma’ana wajen ci gaban Gombe da jin dadin al’ummarta.

Source: Twitter
Ya tuna alamar da aka yi a baya
Ɗan siyasar ya bayyana matuƙar girmama mutanen da ya yi aiki tare da su a baya, yana mai cewa yana godiya kan abubuwan da ya koya.
Ya kuma nuna godiyarsa kan kyakkyawar dangantakar da ya samu a yayin tafiyar siyasar tasa, yana mai cewa abubuwan da suka faru sun ba shi muhimmiyar kwarewa.
Ya ce duk da sabon matakin da ya ɗauka, tafiyar siyasa za ta ci gaba, yayin da kudirinsa na yi wa jama’a hidima zai kasance daram.
A ƙarshe, ya roƙi Allah Ya shiryar da su, Ya kuma ba su nasara a cikin sabon matakin da suka ɗauka na siyasa da hidima ga al’umma domin samun nasarar jam'iyyar APC.
Jigon ADC ya koma layin Pantami
A baya, mun ba ku labarin cewa sakataren yada labarai na ADC na ƙaramar hukumar Gombe ya yi murabus daga jam'iyyar tare da komawa PDP domin mara wa Farfesa Isa Ali Pantami baya.
Ya ce ya sauya sheka ne saboda ya yi imanin Pantami na da ƙwarewa, gogewa da nagartar jagoranci wajen ciyar da Gombe gaba.
Sauyin sheƙar tasa na daga cikin jerin sauye-sauyen siyasa bayan Pantami ya zama ɗan takarar gwamna na PDP a zaɓen shekarar 2027.
Asali: Legit.ng

