Manyan Labarai A Yau
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta musanta batun 'yan daba sun hallaka mutanw biyar bayan rantsar da Sule Garo.
Ana zargin 'yan bindiga da dasa bam a kan hanyar wucewar ababen hawa a jihar Zamfara. Dasa bam din ya jawo rayuka sun salwanta yayin da wasu suka samu raunuka.
Jam'iyyar PDP mai adawa ta rasa daya cikin sanatocin da take da su. Sanata mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Ibrahim Mustapha, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC.
Rahoton hukuma kididdiga ta kasa, NBS ya nuna cewa an samu karin farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 da kashi 20 a watan Maris na shekarar 2026.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya tona asirin masu taimakon 'yan bindiga. Gwamna Radda ya bayyana cewa akwai masu taimakon 'yan bindiga a gwamnati.
Wasu rahotanni da suka yi yawo sun nuna cewa 'ya bindiga sun kai hari a wurin jana'iza a Plateau inda suka kashe mutane. Sai dai, an gano cewa ba gaskiya ba ne.
Majalisar dattawan Najeriya ta sauya sababbin dokokin da ta bullo da su domin hana wasu sanatoci neman mukamai. Ta ce za su saba da kundin tsarin mulki.
Kungiyar Obidient da aka sani da goyon bayan Peter Obi ta rusa tsarinta gaba daya, ta kuma katae duk wata alaka da jam'iyyar LP domin tunkarar zaben 2027.
Daya daga cikin masu neman takarar gwamnan jihar Gombe a APC, Usman Bello Kumo, ya amince da dan takarar maslaha da jam'iyyar ta tsayar domin zaben 2027.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari