Shin da Gaske 'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane a Wurin Jana'iza a Plateau? Gaskiya Ta Bayyana
- Wasu rahotanni da suka yadu sun nuna cewa 'yan bindiga sun kai hari a wani wurin jana'iza a Plateau inda aka ce sun kashe mutane
- Sai dai, an gudanar da bincike wanda ya bankado dalilin da ya sa aka yada batun kai harin na 'yan bindiga
- Hakazalika, rundunar 'yan sandan jihar Plateau ta fitar da sanarwa inda ta yi bayani kan hakikanin abin da ya faru
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - An yada wasu rahotanni da ke cewa 'yan bindiga sun kashe mutane a wajen jana'iza a Plateau.
Sai dai, an gano cewa rahoton farfaganda ce kawai aka yada wadda babu kamshin gaskiya ko kadan a cikinta.

Source: Original
Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
An karyata kisan mutane a wurin jana'iza

Kara karanta wannan
Dan majalisar Amurka ya harzuka kan harin Plateau, ya gayawa Trump matakin dauka kan Najeriya
Ya bayyana cewa bidiyon da ake yaɗawa na yaudara ne kuma ya nuna kamar wasu mutane ne daga cikin taron suka ɗauki hoton.
Ya bayyana cewa:
"Me ya sa za a tada hankali a wurin jana’iza? Mai ɗaukar hoton ne ya ƙirƙiro labarin kuma ya fito da tsarin don ya aika wa kungiyoyin masu ba da tallafi."
"Wane ne nan yake cewa "ku sunkuyar da kai, ku sunkuyar da kai"? A ƙarshe babu wanda ya kawo musu hari amma an riga an sayar da labarin ga ƙungiyoyi masu zaman kansu (NGOs)."
'Yan sanda sun karyata rahoton
Hakazalika, rundunar ’yan sandan jihar Plateau ta yi watsi da rahotannin da ke cewa mahara sun kai wa masu makoki hari lokacin wani taron jana’iza a jihar, inda ta siffanta iƙirarin a matsayin ƙarya da yaudara.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, 5 ga watan Mayun 2026 a Jos, jami’in yaɗa labarai na rundunar, SP Alfred Alabo, ya ce ba a lura da wani hari ba yayin taron jana’izar.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun nuna rashin imani, sun bude wa mutane wuta a wurin jana'iza a Filato
SP Alfred Alabo ya ce an gudanar da taron ne a ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro, inda babban jami’in ’yan sanda na yankin (DPO), jami’an ’yan sanda, da sauran hukumomin tsaro suka halarta tun daga farkon taron har zuwa ƙarshe.
Wani bangare na sanarwar na cewa:
“Iƙirarin an ƙara masa gishiri sosai, ba daidai ba ne, kuma ba ya nuna ainihin abin da ya faru a ƙasa."
Me ya faru a wurin jana'iza a Plateau?
’Yan sandan sun ƙara da cewa an gudanar da binne mutanen cikin lumana ba tare da wani hari daga waje ba kamar yadda wasu rahotanni suka nuna.
A cewar rahoton, an ga wasu matasa ɗauke da makamai da ake zargin mambobin ƙungiyoyin 'yan sa-kai suna harbi a cikin makabartar lokacin jana’izar, lamarin da ya tada damuwa kan yaduwar ƙananan makamai a hannun farar hula.

Source: Twitter
Rahoton ya nuna damuwa kan yadda wasu matasan suka samu makamai, waɗanda suka haɗa da bindigogi ƙirar pistol da sauran makaman da aka ce an gani a bidiyon.
Majiyoyin tsaro sun ce hukumomi suna binciken yanayin da ya sa aka nuna da kuma amfani da makamai a wurin taron.
A halin da ake ciki, kwamishinan ’yan sanda na jihar Plateau, CP Bassey Ewah, ya ƙarfafa tsaro a yankin ta hanyar tura ƙarin jami’ai, ciki har da ’yan sandan kwantar da tarzoma (MOPOL), don hana duk wani tashin hankali.
'Yan bindiga sun kai hari a Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Plateau.
Hare-haren na 'yan bindiga sun yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane shida, yayin da aka kwantar da wasu da dama a asibiti.
Hare-haren sun faru ne daban-daban a dare guda, inda aka bayar da rahoton cewa maharan sun zo ne a ƙasa kuma suna ɗauke da mugayen makamai.
Asali: Legit.ng
