Gwamnatin Tarayya Ta Gano Kuskure, Ta Yi Gyara a Sunan da Ake Kiran Shugaba Bola Tinubu
- Gwamnatin tarayya ta fahimci irin kuskuren da kungiyoyi da kafafen watsa labarai ke yi wajen ambatar cikakken sunan Shugaba Bola Ahmed Tinubu
- Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ya ce wadannan kura-kurai za a iya kauce masu idan aka duba sahihin sunan da ya kamata a hukumance
- Akume ya kuma bayyana yadda ya kamata a rika ambata ko rubuta sunan mai girma shugaban kasa domin kauce wa yawan kura-kuran da ake samu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta nuna rashin jin daɗinta kan abin da ta bayyana a matsayin yawaitar kuskure wajen ambaton cikakken suna tare da mukamin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da wasu ƙungiyoyi da kafafen yaɗa labarai ke yi.
Gwamnatin ta bayyana cikakken sunan da ya kamata a rika kiran Shugaba Tinubu domin kaucewa kura-kuran da ake yi wajen ambaton mai girma shugaban kasa.

Source: Twitter
Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Juma'a, 8 ga watan Mayu, 2026, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.
Sanarwar ta fito ne ta hannun mai ba sakataren gwamnatin tarayya shawara kan harkokin yaɗa labarai, Yomi Odunuga.
Sunan da ya kamata a kira Bola Tinubu
Akume ya ce ya zama dole a yi wannan karin haske bayan da aka samu kuskure wajen ambaton sunan shugaban ƙasa da muƙaminsa a wani rahoto da wata jaridar ƙasa ta wallafa ranar Laraba, 7 ga watan Mayu, 2026.
Ya ce:
“Domin kauce wa ruɗani, sahihin sunan da hukuma ta amince da shi na yadda ya kamata a ambaci shugaban ƙasa shi ne: ‘Mai Girma Bola Ahmed Tinubu, GCFR, Shugaban Ƙasa kuma Babban Kwamandan Rundunar Sojin Najeriya.’”
Gwamnatin tarayya ta yi jan hankali
Akume ya buƙaci jama’a da kafafen yaɗa labarai su riƙa tantance muƙaman jami’an gwamnati kafin wallafawa domin guje wa abin da ya kira kuskuren da za a iya kauce wa da kuma abin kunya a kafafen su da na intanet.
Ya ƙara da cewa ana iya tabbatar da sahihan bayanai ta hanyoyin sadarwa na ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya da suka haɗa da Facebook, Instagram da X, da kuma adireshin imel na hukuma.

Source: Twitter
A cewar sanarwar, Akume ya jaddada cewa irin waɗannan kura-kurai za a iya kauce musu idan aka riƙa neman tabbaci daga sahihan hanyoyin gwamnati kafin wallafa bayanai, cewar rahoton jaridar Punch.
Gwamnati ta yi gyara a digirin girmamawa
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa daga yanzu, ta haramta wa masu wannan digiri da girmamawa amfani da 'Dr.' a farkon sunayensu.
Ministan Ilimi na tarayyar Najeirya, Dr. Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne domin kawo karshen yadda ake bayar da digirin girmamawa ba bisa ka’ida ba, musamman don siyasa da neman kudi.
Asali: Legit.ng

