Hayatudeen: Mai Neman Takarar Shugaban Kasa Ya Riga Atiku Sayen Fom din ADC, Ya Dauki Alkawura
- An samu wanda ya fara sayen fom din neman takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar ADC a zaben 2027
- Mohammed Hayatudeen ya sayi fom din jam'iyyar ADC domin neman tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027
- Mai neman tsayawa takarar shugaban kasar ya bayyana shirye-shiryen da yake da su domin kawo ci gaba a Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mai neman takarar shugaban ƙasa, Mohammed Hayatu-Deen, ya sayi fom ɗin na gani ina so da na tsayawa takara na jam’iyyar ADC, gabanin zaɓubbukan 2027.
Mohammed Hayatu-Deen ya yi alƙawarin magance matsalar rashin tsaro, samar da ayyukan yi, da kuma sauƙaƙa tsadar rayuwa da miliyoyin ’yan Najeriya ke fuskanta.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce Mohammed Hayatu-Deen, wanda shahararren masanin tattalin arziki ne, shi ne mai neman takara na farko da ya karɓi fom ɗin takarar shugaban ƙasa na ADC.
Muhammad Hayatudeen ya karbi dom din ADC
Mai neman takarar shugaban kasar ya karbi fom din ne a hannun sakataren tsare-tsare na jam’iyyar na ƙasa, Prince Chinedu Idigo.
A cewar wata sanarwa daga tawagar bangaren yaɗa labaransa ranar Juma’a, 8 ga watan Mayun 2026, magoya bayansa sun bayyana matakin a matsayin alama mai ƙarfi ta samun karɓuwa ga takararsa.
Maganar Hayatudeen bayan fansar fam a N90m
Jim kaɗan bayan karɓar fom ɗin na Naira miliyan 90, Hayatu-Deen, a cikin sanarwar, ya ce zaɓen 2027 ya kamata ya mayar da hankali ne wajen dawo da daidaiton tattalin arzikin ƙasa da kuma ƙarfafa tsaro, shafin @ADCVanguard a X ya tabbatar da hakan.
“’Yan Najeriya sun gaji da zama cikin fargaba. Sun gaji da kallon yadda kasuwanci ke fuskantar matsi, ayyukan yi na ɓacewa, sannan farashin buƙatun yau da kullum ke tashi fiye da abin da talaka zai iya biya."
“Wannan zaɓen ba zai kasance kan siyasa irin ta da ba. Dole ne ya kasance kan yadda za a tsare al’ummominmu, dawo da amincewa ga tattalin arziki, samar da ayyukan yi masu ɗimbin yawa, da kuma sanya rayuwa ta yi sauƙi ga miliyoyin ’yan Najeriya."
“Ba za mu iya gina arziki a cikin yanayi na tsoro da rashin tabbas ba. Tsaro shi ne harsashin da ake gina kowane tattalin arziki mai ƙarfi a kansa.”
- Mohammed Hayatudeen

Source: Twitter
Wadanne alkawura ya dauka?
Mai neman takarar na ADC ya kuma yi alƙawarin aiwatar da manufofin da za su rage kuɗaɗen gudanar da kasuwanci, tallafa wa ƙananan sana’o’i, samar da ƙarin damammaki ga matasa, da kuma haɓaka tattalin arziki da zai taɓa kowa.
“Na kwashe shekaru da dama ina taimaka wa sana’o’i su bunƙasa da kuma tallafa wa samar da ayyukan yi. Na fahimci abin da ake buƙata wajen gina hukumomi, buɗe kofofin jari, da samar da damammaki masu yawa."
"Najeriya tana da hazaka da damar samun nasara, amma muna buƙatar jagoranci mai kyau da kuma gudanar da aiki da gaske. Wannan ne ya sa na fito don bayar da tawa gudummawar.”
- Mohammed Hayatudeen
Kotu za ta zauna kan shari'ar ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC mai adawa na ci gaba da fuskantar rikici wanda har ya kai gaban kotu.
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar Juma'a, 8 ga watan Mayu, domin sauraron shari'ar rikicin shugabancin jam'iyyar ADC tsakanin Nafiu-Bala Gombe da tsagin Sanata David Mark.
Nafiu Bala Gombe ya shigar da ƙarar ne domin neman kotu ta hana David Mark da Ogbeni Rauf Aregbesola ci gaba da bayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


