Gwamnatin Kano ta Musanta Kashe Mutane bayan Rantsar da Garo, Ta Soki Amnesty

Gwamnatin Kano ta Musanta Kashe Mutane bayan Rantsar da Garo, Ta Soki Amnesty

  • Gwamnatin jihar Kano ta yi martani kan rahotannin da ke cewa an kashe mutane biyar bayan rantsar da Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamna
  • Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya musanta batun tare da yin kakkausar suka kan kungiyar Amnesty
  • Ya bayyana cewa gwamnatin Kano na matukar kokari wajen shawo kan ayyukan daba da dawo da zaman lafiya a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da zargin da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International ta yi na cewa an kashe mutane biyar yayin rantsar da sabon Mlmataimakin Gwamna, Murtala Sule Garo.

Gwamnatin ta bayyana iƙirarin a matsayin ƙarya, yaudara, da kuma nufin siyasa, tana mai jaddada cewa babu wani lamari makamancin haka da ya faru a ciki ko kewaye da gidan gwamnati yayin taron.

Kara karanta wannan

Dan majalisar Amurka ya harzuka kan harin Plateau, ya gayawa Trump matakin dauka kan Najeriya

Gwamnatin Kano ta karyata ikirarin Amnesty kan kashe mutane
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Kwamishinan yaɗa labarai da al’amuran cikin gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a shafinsa na X a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayun 2026.

Gwamnatin Kano ta musanta kashe mutane

Ibrahim Abdullahi Waiya ya zargi ƙungiyar da yaɗa bayanan bogi da kuma lalata amincewar jama’a suka yi mata.

Ya ce reshen Amnesty International na Najeriya ya yi aiki ba tare da ƙwarewa ba wajen haɓaka labaran ƙarya, jita-jita, da kuma labaran yaudara waɗanda za su iya haifar da tashin hankali da ba buƙatarsa a jihar.

Waiya ya buƙaci shugabancin Amnesty International na duniya da su sanya ido sosai kan ayyukan reshensu na Najeriya domin kare mutuncin ƙungiyar.

Gwamnati na kokari wajen yaki da daba

Kwamishinan ya nanata cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ci gaba da jajircewa wajen yaƙi da daba, fadan kungiyoyi, da kuma laifuffukan da suka shafi matasa a faɗin jihar Kano.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya barke a garuruwan jihar Kogi, an rasa rayukan mutane masu yawa

A cewarsa, gwamnati tuni ta ƙaddamar da tsarin “Safe Corridor Kano Model” don sauya hali da kuma tallafa wa matasan da suka tuba daga ayyukan laifi.

Ya bayyana cewa kimanin matasa 2,030 ne aka tantance don shiga cikin shirin a cikin watanni uku da suka gabata.

Waiya ya ƙara da cewa majalisar zartarwa ta jihar Kano ta amince da ba da fiye da Naira miliyan 600 don matakin farko na shirin, wanda ke nufin sauya hali, tallafawa, da kuma mayar da matasa 1,000 cikin al’umma.

Gwamnatin Kano ta musanta ikirarin Amnesty
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Gwamnati ta nuna yatsa ga Amnesty

Ya yi tambaya kan shirun da Amnesty International ta yi game da abin da ya kira “gagarumin ƙoƙari” na gwamnati wajen shawo kan daba da dawo da zaman lafiya a jihar.

Kwamishinan ya tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnati za ta ci gaba da haɗin kai da hukumomin tsaro don kare rayuka da dukiyoyi.

Haka kuma ya yi kira ga mazauna jihar da su goyi bayan binciken da ake gudanarwa kan zargin, sannan su ba hukumomi haɗin kai wajen dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin jihar.

Kara karanta wannan

Daga rantsar da mataimakin gwamna, 'yan daba sun hallaka matasa 5 a Kano

Tinubu ya taya Murtala Sule Garo murna

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya aike da sakon taya murna ga sabon mataimakin gwamnan jihar Kano, Murtala Sule Garo.

Shugaba Bola Tinubu ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan zaɓin da ya yi na daukar Murtala Garo a matsayin mataimakinsa.

Tinubu ya yi wa Murtala Garo fatan alheri a sabon nauyin da aka ɗora masa, tare da ƙarfafa shi kan ya yi aiki kafa-da-kafa da gwamna domin amfanin al'ummar jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng