Zaben 2027: Kungiyar Obidient Ta Canza Suna, Ta Kori Peter Obi da Yunusa Tanko

Zaben 2027: Kungiyar Obidient Ta Canza Suna, Ta Kori Peter Obi da Yunusa Tanko

  • Kungiyar Obidient Movement ta sauya sunanta zuwa Obedient a wani bangare na garambawul da take yi don tunkarar babban zaben 2027
  • Shugaban kungiyar na kasa da kasa, Dr. Barry Avotu Johnson ya sanar da cewa sun yanke shawarar korar tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi
  • Ya kuma bayyana kokar na hannun daman Obi, Yunusa Tanko, sannan ya ce kungiyar ta katse duk wata alaka dake tsakaninta da jam'iyyar LP

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027, harkokin siyasar Najeriya sun sake ɗaukar sabon salo bayan da aka sanar da rushe kungiyar Obidient Movement.

Kungiyar Obidiet ta yi kaurin suna a lokacin harkokin zaben 2023, kuma ta kasance wani dandali na magoya baya 'yan gani kashenin tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi.

Kara karanta wannan

Kotu ta shirya yanke hukunci kan hallacin shiga takarar Jonathan a 2027

Peter Obi.
Tsohon dan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar LP, Peter Obi Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

An kori Peter Obi daga kungiyar Obidient

Tashar Arise News ta ruwaito cewa yayin da Obi ke kokarin sake tsayawa takara a zabe mai zuwa, wasu daga cikin yan Obidient sun sanar da rushe kungiyar gaba daya.

Haka zalika sun kuma sanar da korar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, da kuma na hannun damansa, Yunusa Tanko.

Wadanda suka sanar da matakin sun ce an ɗauke shi ne saboda abin da suka kira “karuwancin siyasa” da kuma amfani da kungiyar wajen cimma muradun kai da samun riba ta kashin kai.

Kungiyar ta sauya sunanta a Najeriya

Sakamakon haka, an sake wa kungiyar suna zuwa Obedient Movement domin raba ta da Obi da magoya bayansa, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Ƙoƙarin jin ta bakin Mista Peter Obi da Yunusa Tanko ta hanyar kiran waya, saƙonnin waya da manhajar WhatsApp bai yi nasara ba, domin ba su daga ko su ka turo amsa ba har kawo yanzu.

Kara karanta wannan

Matasa sun yi cincirindo a gidan Jonathan kan zaben shekarar 2027, sun fadi bukatarsu

Obidient.
Yan kungiyar Obidient yayin da suka fito nuna goyon bayansu ga Peter Obi gabanin zaben 2023 Hoto: Obidient Movement
Source: Twitter

Da yake jawabi a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja domin ƙaddamar da sabuwar kungiyar, shugaban Obedient na ƙasa, Dr. Barry Avotu Johnson, ya ce ba su amince da kowame dan takarar shugaban kasa ba a yanzu.

Ya kuma ce tabbatar da cewa kungiyar ta katse duk wata alaƙa da ke tsakaninta da jam’iyyar LP

A cewarsa, sauya sunan ya zama dole ne bayan da manufofi da akidun asalin kungiyar Obidient Movement suka fara kauce wa hanya bayan zaɓen 2023, musamman lokacin da wasu mutane suka karɓi ragamar tafiyar kungiyar ba bisa ƙa’ida ba.

Peter Obi ya fice daga ADC

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, ya tabbatar da cewa ba zai iya ci gaba da zama a cikin jam’iyyar ADC ba.

Peter Obi ya bayyana cewa ya fuskanci ƙalubale iri ɗaya da waɗanda suka addabe shi a lokacin da yake cikin jam'iyyar LP a baya.

Haka kuma ya wanke tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, inda ya bayyana cewa babu ɗaya daga cikinsu da ya nuna masa rashin adalci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262