An Zubar da Jini bayan Sojoji Sun Gwabza da 'Yan Ta'addan ISWAP a Borno

An Zubar da Jini bayan Sojoji Sun Gwabza da 'Yan Ta'addan ISWAP a Borno

  • Dakarun sojojin Najeriya sun gwabza fada da 'yan ta'addan kungiyar ISWAP a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas
  • Sojojin sun samu nasarar dakile harin da 'yan ta'addan suka kawo a daya daga cikin sansanoninsu bayan an yi kazamin artabu
  • An samu asarar rayuka a tsakanin bangarorin biyu, yayin da sojoji suka fatattaki 'yan ta'addan tare da kwato makamai

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun fafata da 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno.

Rundunar ta bayyana cewa an kashe sojoji biyu yayin da suke fatattakar wani hari da mayakan 'yan ta’adda na ISWAP suka kai a wani sansanin sojojo da ke Magumeri a jihar Borno ranar Alhamis, 7 ga watan Mayun 2026.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'addan ISWAP a Borno
Babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Olufemi Oluyede Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daa jami’in yaɗa labarai na hedikwatar haɗin gwiwar dakarun tsaro (Arewa maso Gabas) na Operation Hadin Kai (OPHK), Laftanar Kanal Sani Uba, ya fitar a shafin X a ranar Juma'a, 8 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

'Ka yi da matata, in yi da matarka,' An kama abokai da ke musayar matansu a Bauchi

Sojoji sun dakile harin 'yan ta'adda

Ya ce ’yan ta’addan sun yi ƙoƙarin kutsa kai cikin sansanin ne cikin dare, inda suka samu damar shiga wani sashe na sansanin.

“Abin sha’awa shi ne, dakarunmu sun yi yaƙi cikin jarumta, inda suka dakile harin ta hanyar kashe ɗimbin ’yan ta’addan."
“Yana da mahimmanci a bayyana cewa ƙarin bincike a yankin ya nuna alamun jini mai yawa, wuraren da aka ja gawarwaki, da kuma gano gawarwakin ’yan ta’adda, wanda hakan ke tabbatar da gagarumin rashi da aka yi wa maharan lokacin harin da aka dakile."
“Dakarun sun kuma ƙwato ɗimbin makamai da alburusai daga hannun ’yan ta’addan da suka tsere, waɗanda suka haɗa da bindigogi masu harbo jiragen sama (PKT), bindigogi ƙirar AK 47, da kuma rumbun harsasai.”

- Laftanar Kanal Sani Uba

Sojoji sun yi artabu da 'yan ISWAP

Lafatanar Kanal Sani Uba ya ce jami’i ɗaya da wasu sojoji sun ji rauni, amma yanzu haka yanayinsu ya daidaita kuma suna karɓar magani.

Kara karanta wannan

An yaye daga ADC, 'yan majalisa 17 sun bi Kwankwaso da Obi zuwa NDC

Ya ce an lalata wasu kayan aiki da gine-ginen wucin gadi sakamakon barin wutar da aka yi yayin kazamin artabun.

Sojoji sun fafata da 'yan ta'addan ISWAP
Dakarun sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Laftanar Kanal Sani Uba ya ƙara da cewa dakarun suna ci gaba da gudanar da ayyuka a yankin domin ƙarfafa nasarar da aka samu, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin tantance irin asarar da aka yi baki ɗaya.

“Wannan hari da ya gaza ya ƙara nuna karsashin yaƙi na dakarun OPHK wajen hana ’yan ta’adda damar gudanar da ayyukansu a faɗin yankin OPHK ke aiki."
“Hedkwatar sojoji ta yaba wa dakarun bisa rawar gani da suka taka a yaƙin, tare da yin kira gare su da su ci gaba da kiyaye wannan karsashi na gudanar da ayyuka.”

- Lafatanar Kanal Sani Uba

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar ragargazar 'yan ta'adda a jihar Borno.

Hazikan dakarun sojoji na rundunar Operation Hadin Kai sun kashe mutane hudu da ake zargi ’yan ta’adda ne bayan sun yi masu kwanton bauna.

Dakarun sojojin sun kuma ƙwato makamai da kayan masarufi yayin wani harin kwanton bauna da suka kai a yankin dajin Sambisa da ke Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng