Majalisa Ta Sauya Sababbin Dokokin da Ta Bullo da Su bayan Surutun Jama'a
- A ranar Laraba, 6 ga watan Mayun 2026 Majalisar dattawa ta yi gyara ga wasu daga cikin dokokin gudanarwarta
- Gyaran da majalisar ta yi na nufin wasu daga cikin sanatoci ba za su samu damar neman manyan mukamai ba
- Sai dai, a yayin zaman majalisar na ranar Alhamis, 7 ga watan Mayun 2026, ta soke wadannan gyare-gyaren da ta yi bayan sun jawo cece-kuce
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta soke gyare-gyaren da ta yi a baya ga dokoki na 2(2) da 3(1) na ƙa’idojin gudanarwarta na shekarar 2023 (kamar yadda aka yi musu gyara), inda ta mayar da tsofaffin dokokin.
Wannan ya biyo bayan damuwar da mambobin majalisar suka nuna cewa wasu muhimman sassa sun yi karo da kundin tsarin mulkin 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima).

Kara karanta wannan
Majalisa: Tirka tirkar da ta jawo zazzafan musayar yawu tsakanin Oshiomole da Akpabio

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa majalisar ta cimma wannan matsayar ne yayin zamanta na ranar Alhamis, 7 ga watan Mayun 2026.
Majalisar dattawa ta kawo sababbin dokoki
Kwanan nan majalisar dattawan ta yi gyara ga ƙa’idojin nata, inda ta taƙaita muƙaman shugabanci na babbar majalisar ga mambobin da suka kwashe aƙalla wa’adi biyu kacal.
Wannan matakin ya rufe ƙofar shiga takarar ga sanatoci masu jiran gado a majalisa ta 11, wadda za a ƙaddamar a watan Yunin 2027.
Sanatoci irin su Hope Uzodimma (Imo), Kabiru Marafa (Zamfara ta Tsakiya), Adams Oshiomhole (Edo ta Arewa), da sauran su waɗanda ake cewa suna zawarcin manyan muƙaman majalisar, sune waɗanda hakan zai iya shafa.
Tsarin gyaran ya haifar da taƙaddama tsakanin shugaban Majalisar dattawa Godswill Akpabio da Sanata Adams Oshiomhole a ranar Laraba, lokacin da shugaban majalisar ya fara karanta rahoton ayyukan majalisar na baya.

Kara karanta wannan
Alkawarin da sabon ministan makamashi ya dauka kan faduwar turakun wutar lantarki
Majalisa ta sauya dokokin da ta kawo
Amma yayin zaman ranar Alhamis, shugaban masu rinjaye na Majalisar dattawa, Sanata Bamidele Opeyemi, ya gabatar da sabon kuduri.
Ya bayyana cewa wasu sassa da aka shigar a ƙarƙashin doka ta 2 karamin sashe na 2 da kuma doka ta 3 karamin sashe na 1 na iya haifar da "saɓani da tsarin mulki da kuma takaddamar da ba a yi niyya ba".
An gano matsala a dokokin
Bamidele ya ƙara da cewa ƙarin bincike kan dokoki da tsarin mulki ya nuna yiwuwar yin karo da sassan kundin tsarin mulkin Najeriya, musamman sashe na 52, wanda ya sa ya zama dole a yi gyaran gaggawa a majalisar, jaridar TheCable ta kawo labarin.

Source: Facebook
Ya ce Majalisar dattawa tana da ikon sake dubawa, canza shawara, da sake dawo da batutuwan da aka riga aka kammala domin kare mutuncin majalisa da al’adun mambobinta.
Daga nan ne majalisar dattawan ta soke shawarar da ta yanke a baya game da gyaran dokoki na 2(2) da 3(1) na ƙa’idojin gudanarwar majalisar, tare da mayar da tsofaffin dokokin da ake amfani da su a baya.

Kara karanta wannan
Gwamnati za ta ba ma'aikata hutun kwanaki 9 domin bukukuwan sallar layya a Turkiyya
Majalisa ta tabbatar da nadin ministoci
A wani labarin kuma, kun ji cewa Majalisar dattawa ta kammala aikin tantance Ministoci biyu da Shugaba Tinubu ya gabatar mata.
Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Ambasada Sola Enikanolaiye a matsayin karamin Ministan harkokin waje.
Haka zalika Majalisar ta amince da nadin Joseph Olasunkanmi Tegbe a matsayin Ministan wutar lantarki kamar yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng