Biliyoyi Sun Ƙaru': Gwamna a Arewa Yana Jin Dadin Kudin Cire Tallafi a Jiharsa

Biliyoyi Sun Ƙaru': Gwamna a Arewa Yana Jin Dadin Kudin Cire Tallafi a Jiharsa

  • Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce jihar yanzu tana karɓar N14 zuwa N16 biliyan a kowane wata, bayan cire tallafin man fetur
  • Sule ya ce kafin cire tallafin, jihar tana karɓar N3.8 zuwa N4.5 biliyan, yayin da ƙananan hukumomi ke samun N1.9 zuwa N2.5 biliyan.
  • Gwamnan ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu, yana cewa sauye-sauyen da ya yi sun samar da ƙarin kuɗaɗen da suka ba jihar damar aiwatar da ayyuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lafia, Nasarawa - Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana karuwar samun kudade da jihar ta yi bayan cire tallafin man fetur.

Gwamnan ya ce sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar sun ƙara wa gwamnatocin jihohi kuɗaɗen da za su gudanar da ayyukan raya ƙasa.

Gwamna ya yaba wa Tinubu kan cire tallafin mai
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga, Gov. Abdullahi Sule Mandate.
Source: Twitter

Gwamna Sule ya yaba wa Tinubu

Kara karanta wannan

Daga sama har ƙasa: Gwamna ya mallakarwa Tinubu ƙuri'un jiharsa a 2027

Sule ya bayyana hakan ne a Lafia, lokacin da yake karɓar baƙuncin ’yan jarida da tawagar yaɗa labaran shugaban ƙasa da ke duba ayyukan gwamnatin tarayya da jiha a jihar, cewar Vanguard.

Ya bayyana cewa kafin cire tallafin, Nasarawa tana karɓar tsakanin N3.8 biliyan zuwa kusan N4.5 biliyan a kowane wata daga rabon kuɗaɗen tarayya, yayin da ƙananan hukumomi ke samun tsakanin N1.9 biliyan da N2.5 biliyan.

Sule ya ƙara da cewa kuɗaɗen da jihar ke karɓa a kowane wata sun ninka fiye da sau biyu bayan cire tallafin man fetur.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta ƙaddamar da ayyuka da dama ba tare da karɓar rance ba, yana mai cewa ya kamata a yaba wa Shugaba Tinubu saboda samar da damar kuɗaɗen da ta ba da damar aiwatar da ayyukan.

Ya ce:

“Dukkan ayyukan da muke gudanarwa a Nasarawa a yau, ba tare da karɓar rance daga banki ba, sakamakon Shugaba Bola da goyon bayansa ne.”
Gwamna ya fadi alherin da yake samu kan cire tallafi
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa. Hoto: Gov. Abdullahi Sule Mandate.
Source: Facebook

Alherin da zuwan Tinubu ya zo da shi

Sule ya ce ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha ya fi nasa kyau, yana mai cewa babu laifi saboda lokacin da aka gina ofishinsa, Tinubu bai kasance Shugaban Ƙasa ba kuma jihar ba ta da irin kuɗaɗen da take samu yanzu.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Buba Galadima ya siffanta Bala Mohammed da rabin gwamna

Ya ce:

“Ga Nasarawa, abin da muke samu yana tsakanin N3.8 biliyan zuwa kusan N4.5 biliyan ga jihar. Ƙananan hukumomi kuma suna samun tsakanin N1.9 biliyan da N2.5 biliyan a kowane wata.
“Bayan cire tallafin man fetur, zan iya gaya muku cewa Nasarawa yanzu tana karɓar matsakaicin N14 zuwa N16 biliyan a kowane wata.”

Sule ya kuma ce ana zarginsa da cewa ya daina yin gaskiya saboda yana yaba wa gwamnati, bayan da a baya yake yawan sukar duk wani abu da bai dace ba.

Gwamna Sule ya bugi kirji kan ayyukan alheri

An ji cewa Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce burinsa shi ne a tuna da shi a matsayin wanda ya fitar da jihar daga mawuyacin hali.

Sule ya ce gwamnatinsa ta inganta hadin kan al’umma, rage tasirin jam’iyyun adawa, tare da kara bunkasa masana’antu.

Gwamnan ya bayyana Nasarawa a matsayin “lu’u-lu’u da ke boye”, yana mai cewa gwamnatinsa ta bude damarmakin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.