Rahoton NBS: Farashin Buhun Shinkafa 50kg Ya Tashi, Ya Karu da Kashi 20 a Najeriya
- Hukumar NBS ta bayyana cewa a binciken da ta gudanar a watan Maris, 2026, farashin buhun tsabar shinkafa 50kg ya tashi da kashi 20.5
- Rahoton na NBS ya nuna cewa matsakaicin farashin buhun shinkafar ya kai N112,00 a watan Maris, daga N92,946 da aka sayar a watan Fabrairu
- Sai dai binciken da aka yi ya nuna farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 ya dawo N60,000 a wasu kasuwanni a sassan Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa matsakaicin farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 ya ƙaru da kashi 20.5 cikin ɗari a watan Maris 2026.
Hukumar NBS ta ce farashin buhun shinkafar ya tashi zuwa N112,000 daga N92,946 da aka sayar da shi a watan Fabrairu, 2026 a wasu sassan kasar nan.

Source: Getty Images
NBS ta bayyana hakan ne a rahotonta na sa ido kan farashin kayan abinci na watan Maris 2026 da ta fitar a ranar Laraba, 7 ga watan Mayu, 2026, kamar yadda Vanguard ta wallafa.
Shinkafa yar gwamnati ta kara tsada
Sai dai binciken da aka gudanar a watan da muke ya nuna cewa a wasu kasuwanni ana sayar da buhun shinkafar gida mai nauyin kilo 50 kan farashin N60,000 duk da tsadar da ake samu a baya-bayan nan.
Rahoton ya kuma nuna cewa farashin buhun shinkafar waje mai nauyin kilo 50 ya ƙaru da kashi 3.06 cikin ɗari zuwa N133,975 a watan Maris daga N110,589 da aka sayar da shi a watan Fabrairu.
Farashin kwai da wasu kayayyaki
NBS ta ce wasu kayayyakin abinci ma sun samu ƙarin farashi a lokacin da aka gudanar da binciken, kamar yadda Punch ta kawo.
Rahoton ya ce:
“Rahoton sa ido kan farashin kayan abinci na watan Maris 2026 ya nuna cewa matsakaicin farashin ƙwai guda 30 ya ƙaru da kashi 2 idan aka kwatanta da watan Fabrairu 2026.

Kara karanta wannan
Bayan abin da ya faru, an haramta wa masu digirin girmamawa amfani da 'Dr' a Najeriya
“Haka kuma, matsakaicin farashin wake mai ruwan kasa kilo 1 ya kai N1,325.85 a watan Maris 2026. Wannan ya nuna ƙarin kashi 1.41 cikin ɗari daga N1,307.44 a watan Fabrairu 2026.
“Haka zalika, matsakaicin farashin albasa kilo 1 ya ƙaru da kashi 1.59 cikin ɗari zuwa N1,153.14 a watan Maris daga farashin watan Fabrairu, 2026."

Source: Twitter
Jihohin da kaya suka fi tsada da araha
Hukumar ta kuma bayyana cewa jihar Taraba ce ta fi kowace jiha tsadar koras na ƙwai, inda ake sayar da shi a farashin N6,999, yayin da jihar Neja ta fi sauƙin farashi da N5,610.04.
Ta ƙara da cewa:
“A bangaren wake mai ruwan kasa kilo 1, jihar Oyo ce ta fi tsada da N1,937.20, yayin da Taraba ta fi sauƙi da N745.
“Haka kuma, matsakaicin farashin albasa kilo 1 ya fi tsada a jihar Abia da N2,115.67, yayin da jihar Kwara ta fi sauƙin farashi da N829.9.”
Manoma na shirin daina noma shinkafa
A wani labarin, kun ji cewa manoman shinkafa 3,500 na shirin barin aikin noma bayan tafka asarar Naira biliyan 93 sakamakon shigo da shinkafar waje.
Wannan bayani ya fito ne daga wani binciken jin ra'ayin manoma na lokacin rani, inda aka tantance manoma 33,507 a jihohi 13 a matakin gwaji.
Rahoton ya nuna cewa manoman shinkafa sun tafka asarar Naira 20,220 a kowace hekta ɗaya a daminar 2025, wnada hakan ya sa suka fara tunanin canza akala.
Asali: Legit.ng

