Lokaci Ya Yi: Tsohon Shugaban Kasa a Afrika, Mogae, Ya Yi Bankwana da Duniya
- An shiga jimami a kasar Botswana da ke Kudancin Nahiyar Afrika bayan rasuwar daya daga cikin tsofaffin shugabanninta
- Tsohon shugaban kasar Botswana, Festus Mogae, ya yi bankwana da duniya bayan fama da rashin lafiya
- Ana ganin girman marigayin kan yadda ya gudanar da jagorancin kasar a lokacin da yake rike da madadun iko
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Gaborone, kasar Botswana - Tsohon shugaban ƙasar Botswana, Festus Mogae, ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayi Festus Mogae wanda ya shugabanci kasar Botswana, ya rasu yana ɗan shekara 86 a duniya.

Source: Getty Images
Tashar BBC ta kawo rahoton cewa shugaban kasar Botswana, Duma Boko ya sanar da rasuwar Festus Mogae a ranar Juma'a, 8 ga watan Mayun 2026.
Festus Mogae ya bar duniya
Duma Boko ya bayyana cewa marigayin ya yi bankwana da duniya ne da safiyar ranar Juma'a, 8 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan
Jakadanci: Fani Kayode ya faɗi dalilin neman Tinubu ya dauke shi daga turai zuwa Afirka
"A yau Botswana tana makokin wani fitaccen jagora kuma mai kishin ƙasa wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga yi wa ƙasarsa hidima."
- Duma Boko
Tsohon shugaban, wanda ya jagoranci Botswana daga shekarar 1998 zuwa 2008, ya kwashe lokaci mai tsawo yana fama da rashin lafiya, rahoton tashar Reuters ya tabbatar da hakan.
A cikin wata sanarwa a watan jiya, gwamnati ta bayyana cewa yana karɓar magani a wani asibiti da ke babban birnin ƙasar, Gaborone, ba tare da bayyana irin rashin lafiyar da yake fama da ita ba.
Festus Mogae, shugaban ƙasa na uku a tarihin ƙasar, ana girmama shi sosai wajen ƙarfafa tsarin tafiyar da tattalin arziki da harkokin mulki na Botswana a lokacin da ƙasar ke samun saurin bunƙasa sakamakon kuɗaɗen da ake samu daga lu’u-lu’u.
Shugaban Botswana ya yabi marigayin
A cikin jawabin da ya yi wa al'ummar ƙasar a ranar Juma'a, Boko ya yaba wa Mogae a matsayin:
"Shugaban da ya tsaya tsayin daka wajen tabbatar da gaskiya, kyakkyawan shugabanci, tattali a fannin tattalin arziki, da kuma ci gaban al'ummarmu."

Kara karanta wannan
Dan majalisar Amurka ya harzuka kan harin Plateau, ya gayawa Trump matakin dauka kan Najeriya
"A ƙarƙashin jagorancinsa, Botswana ta samu girmamawa a duniya saboda shugabanci mai cike da manufa."
- Duma Boko
Duma Boko ya sanar da kwanaki uku na zaman makokin a kasar, inda za a sauke tutoci a matsayin girmamawa ga marigayin.
Mogae ya rike mukamai a Botswana
Kafin ya zama shugaban ƙasa, Mogae ya riƙe manyan muƙamai a gwamnati da suka haɗa da ministan kuɗi, sannan daga baya ya zama mataimakin shugaban ƙasa.
Haka kuma, ana girmamashi kan jagorantar yadda Botswana ta yaƙi cutar kanjamau (HIV/AIDS).
A wancan lokacin, ƙasarsa tana ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi fama da yawan masu cutar a duniya, amma wani gagarumin shirin bayar da magungunan rage kaifin kwayar cutar ya rage yawan masu kamuwa da cutar da kuma mace-mace sosai.

Source: Getty Images
Ko bayan ya bar mulki, ya ci gaba da zama mai fafutukar neman maganin HIV/AIDS a yankin, inda ya matsawa gwamnatoci lamba don bayar da maganin kyauta da kuma matakan hana uwa shafa wa jaririnta cutar.
Ian Khama ne ya gaji Festus Mogae a matsayin shugaban ƙasar Botswana.
Botswana tana ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka da suka fi samun zaman lafiya a fannin siyasa, insa ba a taɓa yin juyin mulki a ƙasar ba, kuma ana gudanar da zaɓubbuka na jam’iyyu daban-daban akai-akai tun bayan samun ’yancin kai a shekarar 1966.
Yayan tsohon gwamna ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa yayan tsohon gwamnan jihar Bayelsa kuma tsohon karamin Ministan man fetur, Timipre Sylva, ya yi bankwana da duniya.
Cif Johnbull Anagha ya rasu ne ranar Laraba, 6 ga watan Mayun 2026, abin da ya jefa iyalai da makusanta cikin alhini.
A cikin sanarwar da aka fitar, an bayyana cewa za a fara gudanar da zaman makoki na kwanaki uku wanda aka fi sani da Duwei Wari domin girmama marigayin.
Asali: Legit.ng
