Atiku Ya Dauko Batun Tsare El Rufai yayin da Ya Kalubalanci Tinubu

Atiku Ya Dauko Batun Tsare El Rufai yayin da Ya Kalubalanci Tinubu

  • Atiku Abubakar ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya umarci ICPC ta saki Nasir El-Rufai idan har yana iya ba EFCC umarni
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce umarnin da Tinubu ya ba EFCC ya karya ikirarin cewa hukumomin yaki da cin hanci suna aiki ba tare da katsalandan ba
  • Atiku ya ce ba za a iya amfani da ikon shugaban kasa bisa zabin siyasa ba tare da yin hakan ga kowa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya kalubalanci Shugaba Bola Tinubu.

Atiku ya kalubalanci Shugaba Tinubu da ya umarci Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka (ICPC) ta saki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

Atiku ya kalubalanci Tinubu
Atiku Abubakar na jawabi a wajen taro Hoto: @atiku
Source: Twitter

Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da hadiminsa, Phrank Shaibu ya fitar a ranar Alhamis, 6 ga watan Agustan 2026, cewar rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya jawo cece kuce bayan ya yi wasu kalamai

El-Rufai na ci gaba da zama a tsare

El-Rufai yana tsare a hannun ICPC tun daga ranar 19 ga watan Fabrairu bisa zargin almundahanar kudi da ake cewa ta faru a lokacin da yake gwamnan jihar Kaduna tsakanin shekarar 2015 da 2023.

A ranar 13 ga watan Afirilu, ICPC ta gurfanar da tsohon gwamnan a babbar kotun jihar Kaduna kan sabbin tuhume-tuhume guda tara da suka shafi zargin damfara da amfani da mukami ba bisa ka'ida ba.

Atiku ya soki ikirarin cin gashin kan EFCC

Atiku ya ce umarnin da Shugaba Tinubu ya ba Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta'annati (EFCC) na bude asusun bankunan gwamnatin jihar Osun ya nuna cewa ikirarin da ake yi na cewa hukumomin yaki da cin hanci suna gudanar da aikinsu cikin 'yanci ba gaskiya ba ne.

A ranar Alhamis, Tinubu ya umarci EFCC ta koma kotu domin ta janye umarnin da aka samu na daskarar da asusun gwamnatin jihar Osun.

Kara karanta wannan

An yi walƙiya: ADC ta nemi Tinubu ya yi wa El Rufa'i yadda aka yi wa gwamnatin Osun

Shugaban ya ce duk da cewa EFCC ta yi aiki cikin ikon da doka ta ba ta, lokacin da aka dauki matakin, kwanaki kadan kafin zaben gwamnan jihar da za a yi ranar 15 ga watan Agusta, bai dace ba.

Atiku ya ce matakin shugaban kasar ya rusa abin da ya kira tatsuniyar cewa EFCC tana aiki ba tare da tasirin gwamnati ba, jaridar The Punch ta kawo labarin.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma yi tambaya kan ikirarin Tinubu cewa EFCC ta samu umarnin kotu kafin ta rufe asusun gwamnatin Osun.

Atiku ya bukaci a saki El-Rufai

Atiku ya ce matakin da Tinubu ya dauka ya haifar masa da nauyin da ya rataya a wuyansa na doka da kuma na dabi'a, wanda bai kamata a rika amfani da shi bisa zabi ba.

"Da yake yanzu ya nuna cewa zai iya ba hukumomin yaki da cin hanci umarnin yadda za su gudanar da wasu ayyuka idan ya ga dama, Shugaba Tinubu yana bin 'yan Najeriya bayanin dalilin da ya sa ba zai iya amfani da wannan iko a batun Malam Nasir El-Rufai ba."
"Idan zai iya umartar EFCC ta dakatar da matakinta a yau, to ba zai iya nuna kamar ba shi da iko kan abin da ICPC za ta yi gobe ba."

Kara karanta wannan

Babbar magana: An gano sababbin hukumomi 2 da aka kafa ba tare da izinin Shugaba Tinubu ba

"Ba za a rika amfani da ikon zartarwa saboda maslahar siyasa ba, sannan a rika kafa hujjar 'yancin hukumomi idan hakan ya dace da fadar shugaban kasa kawai."

- Atiku Abubakar

Atiku ya kalubalanci Tinubu
Atiku Abubakar tare da Malam Nasir El-Rufai Hoto: @atiku
Source: Facebook

Wike ya soki Atiku kan daukar Amaechi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Nyesom Wike, ya yi magana kan zabin da Atiku Abubakar ya yi na Rotimi Amaechi a matsayin abokin takararsa a zaben 2027.

Wike ya ce zabin Rotimi Amaechi a matsayin mataimakin Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na ADC, ba zai kara wa jam’iyyar damar samun nasara a zabe ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng