"Akwai Su a Gwamnati"; Gwamna Radda Tona Masu Taimakon 'Yan Bindiga a Katsina
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi tsokaci kan matsalar da ake fuskanta ta rashin tsaro da kuma ayyukan 'yan bindiga
- Dikko Radda ya bayyana cewa 'yan bindiga na samun mutanen da ke ba su bayanai domin gudanar da munanan ayyukansu
- Gwamnan bai yi kasa a gwiwa ba wajen bayyana cewa har a cikin gwamnati akwai baragurbin da ke taimakon 'yan bindiga
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.
Gwamna Radda ya bayyana cewa akwai "yan leƙen asiri" a cikin gwamnati, hukumomin tsaro, da kuma cikin al'ummomi waɗanda ke bai wa 'yan bindiga bayanai, suna taimaka masu wajen gudanar da ayyukan laifi a jihar.

Source: Facebook
Gwamna Radda ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wata tattaunawa ta musamman da tashar Channels tv.

Kara karanta wannan
Shin da gaske 'yan bindiga sun kashe mutane a wurin jana'iza a Plateau? Gaskiya ta bayyana
Me Gwamna Radda ya ce kan 'yan bindiga?
Gwamna Radda ya bayyana cewa yaƙi da rashin tsaro na fuskantar cikas sakamakon wasu mutane da ke fallasa muhimman bayanan tsaro ga 'yan bindiga.
Ya ambaci sunan wani fitaccen ɗan bindiga da aka sani da sunan Mohammed, inda ya bayyana yadda masu ba da rahoto a cikin gwamnati da al'ummomi ke ba shi bayanan sirri da ke taimaka masa wajen guje wa kama shi.
“Wannan fitaccen mutumin da yake damunmu mun san shi. Shi ne Mohammed; haka sunansa yake. Kowa ya san shi."
"Mahaifinsa, mahaifiyarsa, da kakansa duk a can aka haife su. Amma matsalar da muke da ita ita ce al'umma. Al'ummomin ba sa ba da bayanan da suka dace. Zan iya cewa, ta wata fuskar, wasu daga cikinsu suna taimaka masa."
“Ba boyayyen abu ba ne domin yana samun bayanai. Ranar da na kira taron tsaro na matakin koli a nan gidan gwamnatin jiha kan yadda za a gudanar da aiki da kuma shawo kan lamarin, mintuna biyar bayan kammala taron, har ya riga ya san abin da muka tattauna."
“Akwai 'yan leƙen asiri da ke ba shi bayanai a cikinmu. Hasali ma, ya ma ɓullo da wata sabuwar dabara inda yake tunzura ƙauyuka su yi zanga-zanga ga gwamnati domin su matsa wa gwamnati lamba kada ta kama shi."
“Kuma duk lokacin da aka samu bayanin wani hari kuma jami’an tsaro suka nufi yankin, ’yan leƙen asiri a cikin al’umma za su kira su gaya masa cewa jami’an tsaro suna tafe da kuma hanyar da suke bi, wanda hakan ke ba su damar yi wa jami’an tsaron kwanton ɓauna."
"Don haka, wannan shi ne irin halin da muke ciki. Akwai 'yan leƙen asiri a cikinmu, akwai a cikin hukumomin tsaro, kuma akwai a cikin al'ummomi."
- Gwamna Dikko Umaru Radda
Batun sulhu da 'yan bindiga
Game da batun tattaunawa da 'yan bindiga kuwa, duk da adawar da wasu gwamnoni ke yi ga ra'ayin, Radda ya bayyana cewa kodayake shi kansa ba ya goyon bayan tattaunawa da 'yan fashi, wasu al'ummomi sun nemi izinin tattaunawa da su.
Ya ce ya ba wa al'ummomin damar ci gaba da tattaunawa saboda sun yi amannar cewa hakan zai kawo zaman lafiya.
A cewarsa, ƙananan hukumomin da suka ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan bindiga ba su sake samun hare-hare ba tun daga lokacin.

Source: Facebook
Radda ba zai tattauna da 'yan bindiga ba
To sai dai, Gwamna Radda ya nanata cewa shi kansa ba zai fara tattaunawa da 'yan bindigan da ke daji ba.
Ya ƙara da cewa idan suka tunkare shi don tattaunawar zaman lafiya, zai kasance a shirye ya tattauna, amma sai dai idan hakan zai kasance ta hanyar nuna ƙarfi ne maimakon rauni.
'Yan bindiga sun kashe mutane a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ramuwar gayya a jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma.
Tsagerun 'yan bindigan sun kashe mutane 11 a ƙauyen Gwalgoro da ke karamar hukumar Kankia a jihar Katsina.
An kashe mutanen ne biyo bayan wani harin ɗaukar fansa da ake zargin ’yan bindiga suka kai, sa’o’i kaɗan bayan jami’an tsaro sun hallaka wasu daga cikinsu.
Asali: Legit.ng

