Sanata a Kaduna Ya Sauya Sheka daga PDP zuwa Jam'iyyar ADC
- Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta sake samun karuwa a majalisar dattawa bayan wani sanata ya sauya sheka zuwa cikinta
- Sanata mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Ibrahim Mustapha, ya sanar da sauya shekarsa zuwa jam'iyyar ADC bayan ya fice daga PDP wadda ya lashe zabe a karkashinta
- Ibrahim Mustaoha ya danganta matakinsa na sauya sheka daga jam'iyyar PDP a kan rikicin shugabancin da ya addabe ta
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Sanata mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Ibrahim Mustapha, ya fice daga jam'iyyar PDP mai adawa.
Sanata Ibrahim Mustapha ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC bayan ya raba gari da tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta ce an karanta wasiƙar sauya sheƙar Ibrahim Mustapha ne a zauren majalisar dattawa ranar Alhamis, 7 ga watan Mayun 2026.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ne ya karanta wasikar sauya shekar.
Meyasa ya fice daga PDP zuwa ADC?
Ɗan majalisar ya danganta matakin nasa da rikicin shugabanci da ya addabi jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya, jaridar Leadership ta kawo rahoton.
“Na rubuto ne domin sanar da ku shawarar da na yanke na sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar ADC. Wannan shawara ta biyo bayan rikicin shugabanci da ya shafi jam’iyyar."
“Bayan haka, sakamakon tuntuɓa mai faɗi da na yi da mazaɓata da kuma abokan tafiyata na siyasa, na yanke shawarar shiga jam’iyyar ADC domin ci gaba da harkata ta siyasa.”
- Sanata Ibrahim Mustapha
Sanata ya godewa PDP
Sanata Ibrahim Mustapha ya godewa mambobin PDP bisa damar da suka ba shi na yin hidima a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar.
“Duk da haka, ina so na nuna matuƙar godiyata ga mambobin PDP bisa damar da aka ba ni na yi wa ƙasa hidima. Ina godiya da fahimtarku da haɗin kanku. Karɓi gaisuwar girmamawa ta mafi girma.”
- Sanata Ibrahim Mustapha

Source: Facebook
Sanatoci na sauya sheka
Wannan sauya sheƙa ta ƙara yawan ’yan majalisar da ke barin jam’iyyun adawa a daidai lokacin da ake tsaka da shirye-shiryen siyasa gabanin babban zaɓen 2027.
Bayan wannan sauya sheƙa ta baya-bayan nan, tsarin jam’iyyu a majalisar dattawa yanzu haka yana matsayin: APC tana da mambobi 87, ADC tana da takwas, PDP tana da uku, NDC tana da huɗu, APGA tana da ɗaya, Accord tana da ɗaya, sannan LP tana da ɗaya.
Majalisar dattawa ta soke sauya dokoki
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta sauya sababbin dokokin da ta bullo da su wadanda suka shafi neman manyan mukamai a cikinta.
Majalisar dattawan ta soke gyare-gyaren da ta yi a baya ga dokoki na 2(2) da 3(1) na ƙa’idojin gudanarwarta na shekarar 2023, inda ta mayar da tsofaffin dokokin.
Sauyin ya biyo bayan damuwar da mambobin majalisar suka nuna cewa wasu muhimman sassa sun yi karo da kundin tsarin mulkin 1999.
Asali: Legit.ng

