'Yan Sanda Sun Harbe Shugaban 'Yan Bindiga da Ya Jagoranci Kashe Sarki
- Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta samu gagarumar nasara a binciken kisan Sarkin Ochia, Eze Paulinus Ekwueme, da wasu mutane biyar a jihar Imo
- 'Yan sanda sun kama wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a kisan, yayin da aka kashe wani da ake zargin jagoran ƙungiyar masu aikata laifin a musayar wuta da jami'an tsaro
- Rundunar ta ce ta kwato bindigar AK-47 guda ɗaya, harsashi guda 56 da kuma wata jakar guda uku yayin samamen da aka kai maboyar wanda ake zargin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Imo – Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta samu gagarumar nasara a binciken kisan Sarkin Ochia, Eze Paulinus Ekwueme, da wasu mutane biyar a ƙaramar hukumar Ohaji/Egbema ta jihar Imo.
Rundunar ta ce jami'anta sun kama wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a kisan, yayin da aka kashe wani da ake zargin jagoran ƙungiyar masu aikata laifin a yayin musayar wuta da 'yan sanda.

Source: Twitter
Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Najeriya, CSP Aniete Iniedu, ne ya bayyana hakan ranar Asabar, inda ya ce an samu nasarar ne bayan jami'an tsaro sun samu sahihan bayanan sirri.
An harbe shugaban 'yan bindiga
Iniedu ya ce jami'ansu sun gudanar da jerin samame tsakanin 2 zuwa 6 ga Agusta 2026 domin kamo mambobin wata ƙungiyar masu aikata laifi da ake zargi da hannu a kisan.
Ya ce a farkon ranar 6 ga Agusta, jami'an sun gano maboyar wani da ake zargin jagoran ƙungiyar ne, mai suna Ojiogu Elumah Martin, wanda ake wa laƙabi da “Acid”, a Ohaji/Egbema.
A cewar rundunar, wanda ake zargin ya buɗe wa jami'an wuta, lamarin da ya haifar da musayar wuta. Ya samu raunuka a yayin arangamar kuma daga bisani ya mutu.
An kwato bindigar AK-47 guda ɗaya, jaka guda uku na harsashi guda 56 kirar 7.62mm daga wurin da aka yi artabun.

Source: Original
Maganar kashe sarki
Rundunar ta ce an gano Ojiogu Elumah Martin a matsayin wanda ake zargin jagoran ƙungiyar da ke da alaƙa da harin ranar 10 ga Afrilu 2026.
A harin, an kashe Eze Paulinus Ekwueme, Ochia I na Ochia Kingdom, tare da wasu mutane biyar a kan hanyar Asa/Awara da ke Ohaji/Egbema yayin da suke dawowa Owerri.
Rundunar ta ce tun da farko an kama mutane huɗu dangane da lamarin, yayin da wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a harin suka mutu a arangamar da suka yi da 'yan sanda a baya.
An tura karin sojoji Kebbi
A wani labarin, mun ruwaito cewa Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya tura ƙarin sojoji zuwa jihar Kebbi domin ƙarfafa ayyukan tsaro da ake gudanarwa kan hare-haren 'yan bindiga da garkuwa da mutane.
An tura ƙarin dakarun ne zuwa ƙananan hukumomin Yauri, Shanga da Ngaski sakamakon kutsen 'yan bindiga daga jihohin Zamfara, Neja da Kwara.
Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Babban Hafsan Sojin Ƙasa kan amsa kiran jihar na ƙara yawan jami'an tsaro, yana mai cewa zuwan ƙarin sojojin zai ƙarfafa yaƙi da 'yan bindiga da sauran masu aikata laifi.
Asali: Legit.ng

