Manyan Labarai A Yau
Dan Majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Abuja Municipal/Bwari, Hon. Obika ya bayyana cewa ya canza jam'iyya ne saboda cika buri da manufofinsa na siyasa.
Tsohon Ministan sufuri kuma mai neman takarar shugaban kasa a karkashin inuwar ADC, Rotimi Amaechi, ya sha alwashin gyara Najeriya cikin shekara hudu.
Tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya. Olusegun Mimiko ya nuna goyon bayansa ga Bola Tinubu.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya yi magana kan dalilinsa na fasa sayan kungiyar kwallom kafa ta Arsenal da ke a kasar Ingila.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na LO, Peter Obi ya jaddada cewa matukar aka zabe shi a zaben 2027, shekaru hudu kawai zai yi ya mika wa Arewa mulki.
Tsohon shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya janye daga neman takarar gwamnan jihar Yobe a karkashin inuwar jam'iyyar APC.
Fadar White House ta bayyana cewa Shugaba Donald Trump da takwaransa na China, Xi Jinping, sun amince cewa dole ne a bude mashigar ruwa ta Hormuz.
Shugaba Donald Trump ya gana da shugaba Xi Jinping na kasar China. Xi Jinping ya gargadi Trump kan batun Taiwan, inda ya ce za su yi babban rikici.
Majalisar zartarwa ta jihar Sakkwato ta amince da ware Naira biliyan 5 domin gudanar da wasu ayyukan morr rayuwa da saya wa gwamna motocin sulke.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari