Gwamna Ya Gaji da Alƙawarin Iska, Ya Tura Buƙata ga Sojoji kan Ƴan Bindiga
- Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya bukaci rundunar sojin Najeriya ta kawar da ’yan bindiga da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma
- Gwamnan ya bayyana hakan yayin ziyarar ba-zata da ya kai sansanin sojoji da ke Yauri, inda ya yaba da jajircewarsu wajen kare al’umma
- Ya ce karin sojojin da aka tura Kebbi zai karfafa yaki da ’yan bindiga, musamman a yankin Yauri, Shanga da Ngaski
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kebbi - Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, a ranar Juma’a, ya yi magana game da karuwar hare-haren ƴan bindiga a jiharsa
Gwamnan ya bukaci rundunar sojin Najeriya ta kawar da ’yan bindiga da ke ci gaba da barazana ga rayuka da dukiyoyi a jihar.

Source: Facebook
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ziyarar ba-zata da ya kai wa sojoji a sansaninsu da ke Yauri, inda ya yaba musu saboda jarumtaka da sadaukarwarsu wajen gudanar da ayyukansu, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan
Pantamiyya ta yi rashi, hadimin Pantami ya bar layinsa, ya koma goyon bayan Jamilu Gwamna
Gwamna ya himmatu kan yaki da rashin tsaro
Gwamna Idris ya sake tabbatar da kudurin gwamnatinsa na samar da dukkanin tallafin da ake bukata da kuma kyakkyawan yanayin aiki ga hukumomin tsaro.
Ya ce tsaro nauyin kowa ne, don haka ya bukaci gwamnatocin jihohi su kasance masu ruwa da tsaki wajen tallafa wa gwamnatin tarayya wajen kare al’ummomin da ke cikin hadari.
Ya ce hakan zai taimaka wajen samar da yanayin da zai ba manoma damar komawa gonakinsu cikin aminci domin ci gaba da noma.
Gwamnan ya ce:
"Batun tsaro nauyin kowa ne. Dole gwamnatocin jihohi su kasance masu ruwa da tsaki wajen tallafa wa gwamnatin tarayya domin tabbatar da tsaron yankunan da ke cikin hadari.
“Hakan zai sa yankunan su kasance cikin aminci, ta yadda manoma za su iya komawa gonakinsu domin noma.
“’Yan bindiga na kokarin bata mana suna. Suna zuwa suna kai wa mutanenmu hari. Dole hukumomin tsaro su kawar da wadannan ’yan bindiga, sannan karfin sojoji ya bayyana."

Kara karanta wannan
Tura ta kai bango, an bukaci sojoji su yi zuwa daya su gama da 'yan bindiga a Kebbi

Source: Original
Godiya gwamna da hafsan sojoji
Gwamnan ya gode wa Babban Hafsan Sojin Kasa bisa tura karin rundunonin soji zuwa jihar domin karfafa yaki da ’yan bindiga.
Ya ce tura karin sojojin ya cika bukatar gwamnatin jihar ta neman kara yawan jami’an tsaro a yankunan da lamarin ya fi shafa.
“Na yi farin ciki da yadda kuke gudanar da aikinku. Babban Hafsan Sojin Kasa, tare da goyon bayan shugabannin rundunar, ya amsa bukatarmu ta turo ku nan Kebbi, kasancewarku a nan zai taimaka wajen karfafa ayyukan sauran hukumomin tsaro.
“Yankin Yauri, Shanga da Ngaski na fuskantar kutsen ’yan bindiga daga jihohin makwabta na Neja, Zamfara da Kwara."
- Cewar Nasir Idris
Tattaunawar hadimin gwamna da Legit Hausa
Wani hadimin gwamnan Kebbi, Yahaya Sarki ya bayyana irin kokarin da gwamnan ke yi domin kawo karshen matsalar tsaro.
Ya ce:
"Gwamna yana namijin kokari wurin yaki da rashin tsaro musamman a yankin Yauri wanda ya shafi kananan hukumomin Yauri, Shanga da Ngaski.
"Ya yi kokari wurin karin jami'an tsaro wanda hafsan sojoji ya kawo ziyara domin inganta harkokin tsaro inda ya masu godiya."
Gwamna ya kirkiri sabuwar masarauta a Kebbi
An ji cewa Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya amince da ƙirƙirar sabuwar gunduma a ƙaramar hukumar Suru domin ƙarfafa tsarin masarautun gargajiya.
Haka kuma gwamnan ya ɗaga matsayin Mai Unguwar Tarasa zuwa hakimi bayan raba yankin daga gundumar Kola a ƙaramar hukumar Birnin Kebbi.
Gwamnatin jihar ta ce matakan sun yi daidai da dokar ƙananan hukumomin jihar Kebbi ta shekarar 2008 kuma sun fara aiki nan take
Asali: Legit.ng
