"Shekara 4 Zan Yi," Peter Obi Ya Nanata Alkawarin da Ya Dauka Idan Ya Lashe Zaben 2027
- Tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya nanata alkawarin da ya yi na yin zangon mulki daya idan aka zabe shi a shekarar 2027
- Obi, wanda ya koma NDC kwanan nan, ya ce ba zai kara awa guda a kan shekaru hudu ba ko da kuwa an sanya masa bindiga a kansa
- Wannan dai ba shi ne karon farko da tsohon gwamnan ke fadar hakan ba, ya ce kwashe tsawon lokaci a kan mulki ba shi ke kawo masara ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, ya bayyana cewa wa’adi ɗaya na shekaru huɗu kadai zai yi idan aka zaɓe shi a 2027.
Obi, wanda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar NDC kwanan nan, ya yi ikirarin cewa ko da za a dora masa bindiga a tsakiyar kai, ba zai wuce zangon mulki daya a matsayin shugaban kasa ba.

Source: UGC
Peter Obi ya nanata alkawarin wa'adi 1
Peter Obi ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na News Central TV wadda za a yaɗa a ranar Alhamis.
Ya ce:
"Ina son zama shugaban ƙasa na wa’adi ɗaya ne domin tabbatar da daidaito. Ba zan ƙara ko da rana ɗaya ba bayan shekaru huɗu, koda kuwa za a nuna mini bindiga a kaina."
Peter Obi ya soki manufofin Tinubu
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya kuma soki manufofin tattalin arziƙi na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, ciki har da batun cin bashi da kuma tsadar rayuwa.
Ya bayyana cewa Najeriya karkashin shugabancin Bola Ahmed Tonubu ta shiga ɗaya daga cikin mawuyacin lokaci a tarihinta.
Tun lokacin da ya shiga hadakar adawa ta ADC a watan Yunin 2025, Obi ya ci gaba da jaddada alƙawarin yin wa’adi ɗaya idan aka zaɓe shi.
Dalilin Obi na daukar alkawari
Obi ya ce duk ɗan takara daga kudancin ƙasar da aka zaɓa a matsayin shugaban ƙasa a 2027, dole ne ya kasance a shirye ya bar ofis a ranar 28 ga Mayun 2031.
Wannan, a cewarsa, ya yi daidai da "yarjejeniyar raba madafun iko da ba a rubuta ba" da kuma tsarin karɓa-karɓa.

Source: Facebook
Haka zalika a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a watan Agustan bara, Obi ya jaddada cewa tarihi ya nuna shugabanci nagari ba ya ginuwa a kan tsawon lokacin da mutum ya shafe a kan mulki, face tasirin da ya yi a ɗan ƙanƙanin lokaci.
Peter Obi ya gana da Goodluck Jonathan
A wani labarin, kun ji cewa Peter Obi, ya kai ziyara ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan, yayin da shirye-shiryen zaben 2027 ke kara kankama.
Peter Obi ya bayyana ganawar sirrin da ya yi da Jonathan a matsayin mai ma'ana, inda ya kara da cewa tattaunawar ta mayar da hankali ne kan makomar Najeriya.
Ya ce wannan ziyarar tana daga cikin tuntubar juna da yake ci gaba da yi da masu ruwa da tsaki gabanin babban zaɓen 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

